Rundunar ‘yan sandan jihar Anambra da ke kudu maso gabashin Najeriya ta bayyana sakamakon wani bincike da aka gudanar kan wata mata mai suna Miss Chinyere Awuda, wadda aka gano gawarta a wani wurin wanka da aka yi watsi da ita a harabar otal din Cosmila da ke Awka.
A cewar ‘yan sanda, ba a yi wa Awuda dukan tsiya ba kamar yadda aka yi ikirari a baya. Marigayiyar wacce aka tsinci gawarta a otal din a ranar Litinin, 17 ga watan Yuli, an yi ikirarin cewa wasu masu zuwa bude ido ne suka kashe ta, tare da yi mata dukan tsiya, suka jefar da ita a wani kulob da ke cikin otal din.
Sai dai a wani karin bayani kan lamarin, jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Anambra, DSP Tochukwu Ikenga, a wata sanarwa a ranar Juma’a, ya ce sabanin ikirari na cewa an yi wa marigayiyar dukan tsiya har ta mutu, likitan ya gano babu wata alamar rauni a jikinta.
Rahoton binciken gawar ya nuna cewa nutsewa ta yi wanda yai sanadin mutuwarta. Wannan binciken ya yi daidai da ikirarin cewa matar ta yi kokarin tsira lokacin da ta fada ruwa wanda hakan yasa sai da aka dauki tsawon lokaci kafin a iya gano ta.
Da alama ta fada cikin ruwan har ta Nutse a dalilin sakacin masu kula da wajen. A ci gaba da binciken ’yan sanda, an kama mai kula da wajen domin yi masa tambayoyi yayin da aka tsinto gawar aka ajiye a dakin ajiyar gawa domin a tantancewa.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Anambra, CP Aderemi Adeoye, ya bayar da umarnin a mika takardar karar zuwa babban mai shari’a domin tantancewa da kuma ba da shawara kan shari’a.
Rundunar ‘yan sandan ta bayyana cewa duk wani ci gaba da aka samu za a sanar da jama’a nan gaba. Wannan shari'ar tana nuna mahimmancin bincike mai zurfi da kuma yanke shawara mai tushe a cikin batutuwa irin wannan. Yana da mahimmanci ga duk bangarorin da abin ya shafa su jira bayanan hukuma da bincike kafin yanke hukunci ko yin zargi.