Tarihin Sarkin Kano Muhammadu Abbas - Android Pols

 


Ba a san komai ba game da farkon rayuwar Muhammad Abbas. A lokacin yakin basasar Kano na uku, ya kasance mai biyayya ga ’yan uwansa, sannan ya zama Wambai na Kano bayan Aliyu Babba ya jagoranci Yusufawa zuwa ga nasara. 


Ya raka Aliyu Babba zuwa Sokoto domin yakin kaka na shekarar 1903, lokacin da Turawan Ingila suka kwace Kano. 


Bayan yakin Kwatarkwashi ya jagoranci wani sashe na rundunar Kano da ya mika wuya ga Lugard, saboda biyayyarsa, Lugard ya nada shi Sarkin Kano kuma a watan Mayun 1903 ya tabbatar da shi a matsayin Sarkin Kano


Muhammad Abbas ya kasance Sarkin Kano. Lord Lugard ne ya nada shi sarauta bayan zaman da turawa sukaci Kano a 1903, ya jagoranci sauya masarautun Halifa zuwa masarautun Birtaniyya a karkashin Mallakar Arewacin Najeriya.


Malam Muhammadu Abbas shi ne dan Sarki Abdullahi Maje Karofi dan Sarki Malam Ibrahim Dabo. Malam Abbas mutum ne mai rangwame, mai adalci kuma masoyin jama’a.


A Ranar 2 ga watan Afrilu, 1903, Gwamna Lugga ya dawo daga Sakkwato kuma a ranar ne ya nada Wambai Abbas, ya kuma tabbatar da shí bisa gadon sarautar Kano. Aka yi kasaitaccen biki.


A lokacin bikin, Gwamna Lugga da hannunsa ya mika wa sabon Sarki wuka da takobi, sannan ya bude masa laimarsa. Ita sandar sarautar da Gwamna Lugga ya mika wa Sarki Abbas irin sandar nan ce mai daraja ta daya, kamar wadda suka bai wa sabon Sarkin Zazzau. Daga nan, aka rako Sarki ya shiga gidan sarauta.”


Sarki Kano Abbas mutum ne wanda ya kware a sha’anin mulkin jama’a, mutum mai kaifin hankali da hangen nesa. Ya yi kokarin tabbatar da zaman lafiya a Kano da samun karuwar arziki da wadata. Sarki Kano Abbas ya zama mai biyayya, yana umurtar jama’a da su bi abin da zamani ya kawo.


Tun daga wannan shekara ta 1903 zuwa 1919, Turawa suka fitar da hakimai masu yawa. Hakan ya zama dole, domin su tabbatar da mulkinsu a kan mutane. Ta haka ne za a bi su, mulkin kasa yana hannunsu.


Misali, Sarkin Dutse da Dawakin Kudu da Dan’iya da Dan’isa mai ruwa da dan Danburan Cigari hakimin Minjibir da Birnin Kudu da Sarkin Dawaki ldrisu da Danlawan Amadu da Gurara hakimin Dutse da Turaki Manya da hakimin Kura.


Galibinsu yan’uwan Sarki ne, sai suka ce Sarki ya cike gurabansu, sai Sarki ya nada Umaru Galadima ya nada Salihi Turaki ya nada babban dansa Abdullahi Bayero Ciroma. Wadannan nade-nade duk a farkon zuwan turawa aka yi su.


Tun a farkon mulkinsa, Sarkin Kano Abbas ya kai wa Gwamna Lugga ziyara a hedikwatarsa a Zungeru (Cikin jihar Neja ta Yau). Ya kuma yi wannan ziyara lafiya, ya kare ta lafiya, suka yi muhimman shawarrari da Gwamna Lugga ya dawo gida.


A zamanin Sarkin Kano Abbas, Turawa sun kawo wasu muhimman canje-canje a sarautar Kano. A lokacinsa ne aka kirkiro gundumomi in da aka tuttura masu hakimai da za su kula da su, maimakon tsarin da ake yi a da na dukkan hakimai suna tare da Sarki a cikin birni, sai dai a yi rangadi a dawo. A wannan lokaci ne aka gina wa hakiman gidaje a gundumominsu na mulki inda suka fita daga cikin birnin Kano suka koma kauyuka.


Ta haka aka kekketa manyan kasashe wadanda ‘yan’uwan Sarki suke rike da su a da. Tun a lokacin Sarkin Kano Abbas, Turawan Mulkin Mallaka suka fara kafa makarantun koyarwa na zamani inda suka fara koyarwa ta wasu fannonin addinin Musulunci da kuma na boko, musamman koyar da rubutu da karatu na bakaken Romawa na boko.


Daga cikin mutanen da aka fara koyarwa a irin wadannan makarantu akwai Abdulkadir dan Sarkin Kano Abbas duk da yake kuwa ya girma har ma yana rike da wata sarauta ta hakimi. Amma sai aka buga misali da shi don a tauna tsakuwa, aya ta ji tsoro.


Har wa yau dai a tsare-tsaren da Turawa suka kawo a zamanin Sarkin Kano Abbas yin kasashe na hakimai kamar haka:


> A 1908 Birnin Kudu ta zama hakimi in da aka nada Sarkin Kudu Nuhu.


> Gwaram kuwa wadda a da take rike da Birnin Kudu ta koma cin gashin kanta kawai.


> A 1908 dai kuma aka yi wa Bichi gunduma. Abdullahi Bayero wato Ciroman Kano ya zama farkon hikiminta.


> Dawakin Tofa kuma kasar Madaki Usaini ta zama gunduma ita kadai.


> A 1916 Gwarzo ta zama gunduma a karkashin Sarkin Dawaki Maituta Muhammadu Nata’ala.


> Karaye kasar Sarkin Karaye Usman ta koma ita kadai.


>Rano kasar Autan Bawo ta koma ita kadai a matsayin Gunduma.


> A 1908 Tudun Wada ta zama gundüma kuma Dankadai ya zama hakiminta na farko.


> A 1908 dai kuma aka hade Lardin Kano da Katsina da Katagun da Kazaure da Daura da Gumel da Hadeja da Misau da Jama’are da Ningi. Aka mayar da Kano ta záma cibiyar mulkinsa.

Amma daga baya an dauke Katagum da Misau da Jama’are da Ningi suka koma Bauchi wadda ta zama cibiyar mulkinsa


Haka kuma a wajen 1911 jirgin kasa ya iso Kano a dai zamanin Sarkin Kano Abbas inda mutanen Kano masu yawa suka dinga fita zuwa kallon sa a Dan’agundi.


A zamanin Sarkin Kano Abbas ne aka yı wani babban taro cikin shakara ta 1912. A wannan shekarar ne kuma aka fara gina kasuwanni cikin tsarin layi-layi, maimakon rumfuna barkatai babu tsari, aka karu da ni’imomi masu yawa.


Sarkin Kano Abbas kuma ya sami yan majalisa, malamai masu gaskiya da tsoron Allah wadanda kuma suka yarda da abin da Allah ya kawo dangane da zamani su ne kuma:


A Zamanin sarautar Sarkin Kano Abbas ya taba kai ziyara kabarin mahaifinsa, Sarkin Kano Abdullahi Maje Karofi da yake a garin Karofi. Sarkin Kano Abbas ya yi wannan tafiya ne tare da amincewar Gwamna Janar, wato Gwamna Lugga. Sarki ya je ya yi wannan ziyara ya dawo lafiya.


Mulkin Sarkin Kano Abbas ya sami nasara sosai, Kano ta Kara bunkasa ta kowane nau’i na rayuwa. Jama’a sun saki jiki sosai suka ci gaba da harkokin cinikayyarsu Noma da kiwo suka dada bunkasa, kuma ga shi babu sauran yaki, Turawan Mulkin Mallaka Sun kuma hana bauta. harkoki da ma’amaloli, na tsakanin Kasa da kasa suka dada ingantuwa.


Kano ta sami arziki da alhairi su na ta bullo mata ta kowane gefe.


Sarki Kano Abbas Shi ne mahaifin Sarkin Kano Muhammad inuwa Wanda yayi sarauta ta watanni 6 bayan murabus din Sarkin Kano Muhammadu Sunusi na 1.


Allah ya yi wa Sarkin Kano Muhammadu Abbas Maje Nasarawa rasuwa a shekara ta 1919.


Madogara


Palmer, Herbert Richmond (1908). "Kano Chronicle". Journal of the Royal Anthropological Institute of Great Britain and Ireland.


Al'ummar Hausa


Saliadeen Sicey ✍️

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post