Victor Hugo Sosa, Magajin garin San Pedro Huamelula a ƙasar Mexico, ya auri kadan ne don gudanar da tsohuwar al'adar da aka shafe shekara 230 ana yi.
Mutanen garin sun yi imanin cewa aure tsakanin mutum da kadan zai kawo alkairai kamar damuna mai albarka da kyakkyawan amfanin gona.
Dubban jama'a ne ke ta bayyana ra'ayoyinsu akan wannan labarin, inda wasu ma ke bayyana cewa ko dai mutumin yana da tabin kwakwalwa ne, wasu kuwa na cewa hakan ai ba abin mamaki bane domin ba wannan Karen farko da dan adam ke aurar dabba ba.