Juma'a Mai Zuwa Mawaki Ado Isah Gwanja Zai Sake Sabon Aure




Bayan Shafe Shekaru biyu da rabuwar matarsa taking farko an sanar da ranar da zai sake yin wani auren Karo na biyu. 


Shafin Hausa Film Magazine shine ya rawaito labarin inda suka bayyana cewa a ranar juma'a mai zuwa ne za'a daura auren Ado Gwanja. 


Za a ɗaura auren sa da sabuwar abar ƙaunar sa mai suna Maryam Zubair Muhammad Paki a ranar Juma’a, 21 ga Yuli, 2023, a Masallacin Juma’a da ke cikin Jami’ar Yusuf Maitama Sule (Northwest University), Kano.


Yayan Ado Gwanja, wato Alhaji Sa’idu Gwanja, shi ne ya ba da sanarwar ɗaurin auren a guruf ɗin ‘yan fim ta ‘MOPPAN Associates’.


Amma Alhaji Sa’idu ya ce: “Idan ba a samu damar zuwa ba a yi mana addu’a, mun gode.” 


Mujallar Fim ta ruwaito cewa, a shekarar 2021 ne mawaƙin ya rabu da matar sa Maimunatu Ɗan’auta, wadda su na ‘ya ɗaya da ita mai suna Asiya (Balaraba).


Ya zuwa yanzu dai ita Maimunatu ba ta samu yin wani auren ba tukuna.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post