Abba El-Mustapha1 dai guda ne daga cikin jaruman fina-finan Hausa na Kannywood wanda ya jima a tsarin siyasar Kwankwasiyya.
Daman dai tuni hankula suka karkata kan wanda za'a bawa hukumar, yayin da wasu ke tunanin za'a bawa Sunusi Oscar 442, kasancewar yana cikin na gaba-gaba a sha'anin siyasar ta Kwankwasiyya a Kannywood.
Wasu daga cikin jaruman Kannywood dai sun sha fuskantar dauri a gwamnatin baya, abinda aka alakanta da yadda ake zarginsu da nuna zazzafar adawar siyasa ga tsohon gwamna Abdullahi Umar Ganduje na APC a wancan lokaci.