Farashin Sadaki Na Sai ya kai Naira biliyan 11 saboda har yanzu ni budurwa ce Babu Namijin Da Ya sanni

 


Lauya Ifunanya Excel, wata ‘yar Najeriya ce, kuma ma'abociyar shafukan sada zumunta, ta haifar da cece-kuce a yanar gizo bayan da ta bayyana cewa farashin sadakinta ya kai dala miliyan 15 a dolar Amurka, wanda ya haura naira biliyan 11.



Ifunanya, wacce ta shahara da bayyana ra’ayoyinta, wasu lokutan kuma kan haifar da cece-kuce, ta bayyana hakan ne a shafinta na Twitter, inda ta bayyana cewa tsadar sadakin ta ya biyo bayan kasancewarta budurwa da babu namijin da ya taba saduwa da ita.


Tun bayan da ta yi sanarwar ake ta samun ra’ayoyi mabambanta, inda wasu ke nuna rashin tunanin budurwar, yayin da wasu kuma ke kare hakkinta na gindaya wa kanta sharudda.



Wasu dai sun nuna shakku kan ikirarin Ifunanya na cewa ita budurwa ce har yanzu, yayin da wasu ke ganin cewa tsadar sadakin nata ta fada ne kawai don ta jawo cece-Kuce.


Yanzu dai abin jira a gani ko za ta sami mai neman auren da zai biya makudan kudade domin aurenta.




Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post