Darakta Hassan Giggs Da Matarsa Jaruma Muhibbat Abdulsalam Sun Cika Shekara 15 Da Aure




Muhibbat Abdulsalam wacce tsohuwar jarumar Kannywood ce a shekarun baya da mijinta Darakta Hassan Giggs sun cika shekara 15 da aure. 


A wani sako da ya wallafa a shafinsa na Instagram Hassan Giggs ya bayyana yadda suke cikin farin ciki shi da matarsa da yayan su da suka shafe shekara 15 cikin aminci da soyayya. 


Itama Muhibbat Abdulsalam ta bayyana hakan a shafinta na Instagram inda take Yiwa Allah godiya tare da godiya ga iyayensu domin addu'ar su ce ta kawo su har wannan shekarun. 


“Allah na gode maka da ka ba ni ikon zama da miji na na tsawon wannan shekaru.


“Ya Allah na roƙe ka don darajar Manzon ka Allah ka sa mutuwa ce za ta raba mu. Ya Allah ka yi wa zuri’ar mu albarka.”


Auren Giggs da Muhibbat, wanda aka ɗaura a ranar 28 ga Yuni, 2008, ya na daga cikin aurarrakin ‘yan fim da ake ba da misali da su na yadda su ka yi shekaru masu yawa su na zaune lafiya ba tare da sun rabu ko kuma an ji kan su ba.


Allah ya albarkaci auren da kyawawan ‘yan mata guda uku.









Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post