Ranar Lahadi aka yi taron bikin mawaƙin nan Abubakar G-Fresh da amaryarsa Sadiya Haruna fitacciyar mai amfani da kafafen sada zumunta a Arewacin ƙasar nan.
Dama tun a kwanakin baya ne aka ɗaura aurensu amma ba a yi taron shagalin biki ba sai a Lahadin nan.
Shagalin bikin dai ya haifar da cece-kuce a kafafen sada zumunta saboda rashin ganin wadda ta yi uwar amarya wajen shirya bikin wato Jaruma Rashida Mai Sa'a a wajen taron.
Sai dai an ga fuskar Jaruma Teema Makamashi wadda ita kuma suka daɗe suna taƙun saƙa da amarya Sadiya.
Me zaku ce?