Ana Jimamin Mutuwar Auren Tsohuwar Jarumar Kannywood Wasila Isma’il - Android Pols




Labarin mutuwar auren tsohuwar jarumar Kannywood Wasila Isma’il da mijinta Al-Amin Ciroma ya tayar da hazo a kafafen sada zumunta na zamani. 


Ana ganin auren tsofaffin jaruman na daya daga cikin auren da aka yi a masana'antar Kannywood da yai karko tsawon shekaru. 


Shafin Film Magazine ya tabbatar da rabuwar auren Jamila Ismail da Al-Amin Ciroma bayan tuntubar makusantan jaruman. Wani rahoto kuma yai tabbatar da cewa auren ma ya kai kusan wata biyu da mutuwa. 


Sai dai babu wani takamaimen bayani kan musabbabin rabuwar auren nasu duk da tuntubar su da aka yi domin jin Karin bayani. 


Wasila da Ciroma sun haifi 'Ya'ya biyar mata uku maza biyu. 


Kafin rabuwar auren nasu a shekarar da ta gabata suka yi murnar cika shekaru 20 da aure cikin walwala da kwanciyar hankali. 






Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post