Aisha Humaira ta wallafa bidiyon wata Dankareriyar Mota da aka yi mata kyautarta don murnar zagayowar ranar haihuwarta.
Cikin harshen Turanci ta yi rubutu kamar haka a jikin video motar da table wallafa;
"I received this as my birthday gift, Alhamdulillah. He buy me this car Fisabilillahi, Pols ku sanya shi a addu'a Allah ya biya Masa bukatun sa".
Ta kuma kara da cewa 25/07: nake yin birthday amma bana celebrating ina karbar gifts a wajen wanda suka san date din.
Wannan sune sakon da Aisha Humaira ta wallafa akan bidiyon motar da aka bata kamar yadda za ku gani a bidiyon, sai dai bata bayyana sunan mutumin da yai mata kyautar ba.
Ga cikakken bidiyon.
Shin wane fata za ku yiwa jarumar? Ku bayyana mana ra'ayoyin ku.