An Gano Jariri Kwance A Bayan Mahaifiyarsa Awa 24 Bayan 'Yan Bindiga Sun Kashe Ta


An gano wani yaro dan wata bakwai mai suna Habibu yana barci a bayan mahaifiyarsa sa’o’i 24 bayan wasu ‘yan bindiga sun harbe ta a hanyar Pandogari zuwa Allawa a karamar hukumar Shiroro ta jihar Neja. 


An tattaro cewa ‘yan bindiga sun tare hanyar Pandogari zuwa Allawa ana gobe Sallah, inda suka harbe fasinjoji shida, ciki har da wata dalibar SS 2 na Kwalejin Kimiyyar Mata ta Maryam Babangida da ke Minna, Hauwa Aliyu da mahaifiyar jaririn har lahira.


Shugaban Majalisar Matasan Lakpma Jibril Allawa ya tabbatar wa Jaridar Aminiya faruwar lamarin.


“Abin mamaki, jaririn yana daya daga cikin wadanda suka tsira daga harin da aka kashe mutane shida. ‘Yan banga da suka je washegarin kwashe gawarwakin wadanda abin ya shafa sun gano jaririn yana barci a bayan mahaifiyarsa, ”in ji Allawa. 


“Lamarin ya faru ne a ranar 27 ga watan Yuni, kuma mutane shida sun rasa rayukansu. Maryam ta kira ta sanar mana za ta zo gida don yin Sallah. Muka ce mata ta koma makaranta ta yi Sallah a can amma ta dage cewa tana son ta zo gida ta yi biki tare da mu.


Wani matashi mai suna Abubakar Ismail, mai shekaru 16, wanda ya samu raunuka a kirjin sa, ya yi nasarar gudu daga nesa kafin a ceto shi, kuma yanzu haka yana samun kulawa a asibiti.

Wannan itace mahaifiyar Yaron da aka kashe


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

1 Comments

Previous Post Next Post