Labari dake fitowa daga cikin garin Bauchi a wata unguwa da ake kira Dumi wata mata ta halaka mijinta ta hanyar caka masa wuka suka uku a kirjinsa.
Kamar yadda ta bayyana wa 'yan sanda masu bincike, tace cacar baki ne ya shiga tsakaninta da mijinta, sai da ta bari sun kwanta a kan gadonsu na Sunnah da nufin za su yi bacci bayan kammala cacar bakin, sai ta dauko wuka ta caka masa a kirjinsa wanda hakan yayi ajalinsa.
Matar mai suna Maimunatu Sulaiman 'yar Shekara 21 ta kashe mijinta mai suna Aliyu Muhammad a daren Alhamis.
Yanzu haka tana nan a sashin binciken manyan laifuka na 'yan sanda State CID Bauchi, idan an kammala hada bincike za'a gurfanar da ita a Kotu
Labarin dai ya jawo tafka muhawara sosai a shafukan sada zumunta.