Ba kasafai za ka samu bera yana yin rayuwa a inda mage take zauna ba, duk inda age take ba za ka taba ganin bera ya zauna lafiya ba. Sai dai a iya cewa a kasar Saudiya lamarin ya sha bamban domin kuwa tsakanin mage da bera kowa rayuwarsa yake yi ba tare da cutar da wani ba.
Ku Kalli wannan video ku ga abin mamaki yadda Mage take tsince-tsince a bola tare da Bera kuma babu wanda ya shiga harkar wani.