Labari Da Dumi-Dumi na nuna cewa: Sanata Godswill Akpabio ya lashe zaben shugaban Majalisar Dattijai ta 10 a zaben da sababbin 'yan majalisar sukayi a safiyar yau Talata.
Sanata Akpabio wanda ya fito daga jihar Akwa Ibom ya kada abokin takarar sa Sanata Abdulaziz Yari, tsohon gwamnan jihar Zamfara da kuri'a - 63 yayin da Abdulaziz Yari ya samu kuri'a - 46.
Sanata Barau Jibril daga jihar Kano ne mataimakin shugaban majalisar dattijan Nigeria yanzu.
Wanne irin fata kuke yiwa sabuwar majalisar dattijan Nigeria?