Yanzu-Yanzu Kotu Ta sallami Yunusa Yellow Daga Gidan Yari Bayan Shafe Tsawon Lokaci - Android Pols


Masha Allah yau Yunusa Yalo ya shaki iskar ‘yanci bayan tsawon shekaru a daure. Wannan 'yar manuniya ce dake tabbatar da cewar wuya bata kisa kuma zakaran da Allah ya nufa da cara ko ana muzuru ana shaho sai Ya yi.


Shi dai Yunusa Yellow ana zarginsa da cewar ya yaudari wata budurwa daga jihar Anambra ya kawo ta jihar kano har ya aureta kuma yasa ta karbi addini Musulunci. 


Wanda hakan yasa akaita shari'a har tsawon zuwa tsawon lokaci daga Karshe dai aka yanke masa hukunci shekara 25 a gidan yari. Sai dai ba yau kuma matashin ya samu fita daga gidan yari. 


Allah yasa Mu gama da duniya lafiya, Allah ya kiyashe mu da mummunar kaddara.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post