A shekarun baya-bayan nan, an samu ƙaruwar mata baƙaƙen fata masu kwalliya da gashin da aka haife su da shi.
Wannan na nufin gashin da ba a shafa mai (shanfo) ko 'relaxer' ba, sannan ba a yi amfani da ko wane nau'i na ƙarin gashi ba saɓanin yadda aka sani a baya.
Kusan a iya cewa wani gangami ne da ba a san daga inda ya fara ba da ya zaburar da mata baƙar fata da dama daina shafa relaxer a gashinsu.
Ko a shafukan sada zumunta musamman a shafin Youtube, akwai ɗimbin bidiyo kan yadda mata za su kula da gashinsu da aka haife su dashi, da bayanai kan yadda za su daina shafa relaxer ga masu shafawa.
An ƙirƙiri maudu'i da dama kamar #naturalhair da #naturalhaircare #africanhair da dai sauransu a shafukan Twitter da Instagram don tattaunawa kan yadda za a kula da gashin baƙar fata.
Ana iya cewa wannan gangami ba mata kawai ya shafa ba, har maza ma don kuwa yanzu yayin tara ƙasumba ne ke tashe.
A iya cewa ma tara ƙasumba ya zama wani salo na ado ga samari da matasa a wannan zamanin.
Dokta Fatima Abdullahi, likita kuma ƙwararriya a ɓangaren kula da gashin mata ta ce akwai sindarai da dama masu yi wa jiki illa a cikin man relaxer.
"Akwai wani sindari da ake ce wa Lye a cikin man relaxer, yana da illa sosai. Bincike ya gano cewa yana iya shiga cikin jiki ta fatar kanta idan ta shafa wa gashinta," a cewarta.
Ta ce shi ya sa ya fi dacewa mace ta riƙa gyara gashin da Allah ya yi mata, ta kula da shi da mayyuka masu kyau kuma wanda suka dace da gashinmu na ƴan Afrika.
Dokta Fatima ta ce son shafa wa gashin man relaxer ga mata baƙar fata ya samo asali ne a batun da ake cewa gashinmu na da ƙarfi don haka ba a iya kula da shi yadda ya dace.
Ya ce "Mutane da yawa na tunanin cewa sai an shafa wa gashinmu relaxer ne yake iya laushi, ko kuma shi ne zai sa gashinsu ya yi kyau."
"Amma akwai yadda idan kina kula da shi zai yi laushi sosai ba tare da kin shafa relaxer ba," a cewar Dokta Fatima.
Sannan ta ce an nuna cewa shi gashin baƙar fata ba ya kyau sai idan an miƙar da shi, wato da relaxer ko da wasu sinadarai na miƙar da gashi.
Ya za ku kula da gashin kanku da na gemu?
Dokta Fatima ta ce abin da baƙar fata ba su sani ba shi ne amfani da ruwa a kai na taka muhimmiyar rawa a ingancin gashin kai da na gemu.
Ta ce ya kamata ya zama babban abokin mu'amala wurin kula da gashi.
Ta ce "Akwai matan da suke ganin kamar zuba wa gashinsu ruwa yana lalata gashin ne. Saɓanin haka, ruwa shi ne babban abokin irin gashinmu. A ƙalla ya kamata mace ta zuba ruwa ko ta wanke gashinta sau biyu a mako guda.
"Musamman idan kina yawan gumi, wanke kai sau biyu ko uku a mako ma bai yi yawa ba. Idan ba ki yawan gumi ko kin fiye zama da na'urar sanyaya ɗaki ko sau ɗaya a mako ma ya wadatar.
"Ruwan zai taimaka wajen tsaftace fatar kan sannan zai ƙara wa gashinta lafiya da laushi, ya yi kyau kuma ta ji dadin gyara shi," in ji ta.
Ta ce yadda mace za ta kula da fatar jikinta haka ya kamata ta kula da fatar kanta.
"Akwai matsaloli da ka iya faruwa idan ba ki wanke fatar kanki yadda ya kamata. Kina iya samu ƙwarƙwata ko amosani (dandruff) ko ma ƙyasbi."
Sannan ta ce akwai wasu mayuka na musamman da aka yi su don gyaran gashin baƙar fata. Waɗannan mayukan na taimaka wa gashi wajen yin laushi da kara tsawo sosai.
Haka kuma, ta ce akwai ɗabi'un da muke yi da ke sa gashinmu karyewa ko rashin tsawo yadda ya dace.
"A baya, mun saba kawai idan za mu kwanta bacci ba ma kula da irin rigar matashinmu ko irin ɗankwalin da za mu ɗaura a kanmu. Shi ma wannan yana shafar gashi.
"Kamata ya yi mu riƙa ɗaura dankwali ko mu sa hular da aka yi da yadin 'silk' - yadi mai santsi saboda shi ba ya busar da gashinmu," in ji ƙwararriyar.
Ta ce amfani da rigar filo da aka yi da irin wannan yadin mai santsi ma zai taimaka wajen inganta lafiyar gashinmu.
"Gashin da ya bushe ya fi saurin karyewa, kuma idan gashi na yawan karyewa ba zia yi tsawo ba" ia cewar Dokta Fatima.
Dokta Fatima ta ce yin kitso a matse shi tsan-tsan na lalata gashi.
"Akwai kitson zare da ake yi a daure shi da karfi ko a kama tushen gashin a matse shi kai haifar da tsittsinkewar gashi. Wani lokacin ma tun daga tushen gashin yake fita, idan ba a ayi hankali ba sai ya haifar da sanƙo musammana a gaban kai," in ji ta.
Haka kuma, ƙwararriyar ta ce yawan amfani da na'urar busar da gashi kamar 'hand dryer' da mata ke amfani da shi na lalata gashi. Ta ce wannan zafin na yi wa gashi illa shi ne za a ga gashi ya ƙi yin kyau sai dai ya yi ta lalacewa.
Yawan taje gashi ma na haifar da karyewar gashi a cewar Dokta Fatima.
Ta ce ba ko yaushe ne idan mace ta wanke gashi za ta taje shi ba, wani lokaci tana iya sharce shi da yatsun hannunta kawai ba sai ta sa urya ko kum ba.
Dokta Fatima ta ce matuƙar dai ana wanke gashi yadda ya dace kuma ana shafa man da ya dace, sannan an bi shawarwarin da ta bayar, ba a buƙatar sa man relaxer, mace za ta ga gashinta ya yi taushi kuma ba ya wahalar sarrafawa, haka su ma maza masu son ajiye ƙasumba.