Tattaunawar jaruma Hadiza Gabon ta janyo cece-kuce a social media - Android Pols - Android Pols - latest news, natural remedies, and entertainment

Tattaunawar jaruma Hadiza Gabon ta janyo cece-kuce a social media - Android Pols

 


Ana cigaba da cece-kuce a dandalin sada zumunta, akan batun tattaunawar da jarumar masana'antar shirya finafinan Hausa ta Kannywood, Hadiza Gabon, ke gudanarwa a shafin YouTube, tana gayyato abokan sana'ar ta, tare da yi musu tambayoyi masu zafi, wadanda wasu ganin tambayoyin sun fita daga kwarewar aikin jarida, don kuwa akwai wata jaruma da har sai da ta zubda hawaye a dalilin tambayoyin nata. 


Hadiza Gabon ta sanyawa shirin ta suna "Gabon's Room Talk Show" wanda a baya bayan nan ta tattauna da mawaÆ™i El-Mu'az, tayi masa tambaya akan alaÆ™arsa da wata abokiyar sana'arsu, lamarin da ya fusata mawaÆ™in, har shima ya jefa mata wasu tambaya akan sana'ar da ta keyi da kuma yadda take samun kuÉ—i. 


Marubuta a shafin Facebook na cigaba da bayyana ra'ayoyinsu akan batun, inda mafi yawa ke sukar tsarin da jaruma Hadiza Gabon ke bi wajen yin tambayoyi ga baÆ™in ta, harma wasu na ganin ya kamata ta nemo kwarewar aikin jarida, domin tattaunawar ba iya ita kadai da baÆ™in ta ke gani ba, Duniya ce ke kallon su. 


Menene ra'ayin ku? 

Related Posts:
Previous article
Next article

Leave Comments

Post a Comment

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel