Amarya Ki Sani; kamar yadda mutane suke Kai mamaci cikin kabari su tafi su barshi cikin kabarinsa haka iyaye suke kai amarya gidan minjita su tafi su barta cikin dakin aurenta.
Amarya ki nutsu, gabanki ya daina faduwa saboda mijinki ba mai cutarwa bane, farin ciki yazo miki dashi, Wanda yake maida budurwa ta koma uwa bayan lokaci kadan.
Kada Ki Firgita Da Yana Da Mata, Ki Zama wayayyar Mace A Gidan Mijinki
Wayayyun mata kanana ko manya, kishi dasu yana da wahala. Idan mace ita ba wayayya bace ko in ce idan bata dage ba, domin kwace Mata miji ba wuya zai yi ba, saboda wayayyar mace ba ta jin kunya ko girman kan yiwa mijinta duk wani abu na farantawa. Saboda haka amarya ki zama wayayyar mace.
Idan Aka Samu Wayayyar Yarinya Tuni Zata Danne Manyan Mata A Gurin Miji.
Haka ma babbar mace wayayya kishi da ita yana da wahala, domin tana gyara jikinta tana kuma tattalin mijinta, abinda zai sawa abokiyar zamanta tunanin wai me wance take yiwa oga ne yake irin wannan rawar jikin?
Ko wata kasar zashi da ita yake tafiya, don Allah kema zama wayayya a gurin mijinki.