Wata mata tana baiwa matan aure shawara cewa idan har kinsan mijinki yana fita zuwa kallon Kwallo da dare to ki rufe kofar gidan kuma ki kashe wayarki ki bar dan iska ya kwana a waje.
Matar mai suna Xahrau ta wallafa hakan ne a shafinta na Twitter wanda ya jawo aka tafka muhawara sosai.
Sai dai da yawa daga cikin masu yin tsokaci sun yi ala-wadai da shawarar da ta bayar ga mata wasu kuwa sun yi maraba da abinda ta furta.
Shin kuna ganin shawarar da ta baiwa mata ta yi ko kuma akwai gyara? Muna dakon ra'ayoyin ku.