Sharif-uddin (Ko Sharif-iddin) Khalifa, Yaro ne mai ban al'ajabi , An haife shi a Arusha, a Arewacin Tanzaniya (wata ƙasa a Gabashin Afirka), a cikin Disamba 1993. Malaman Addinin Musulunci tsiraru ne a Tanzaniya kuma harshen Larabci Bai yadu a kasar Tanzaniya Sosai ba. Iyayensa Kiristocine Ya Darikar Katolika. Yarensu na Asali Swahili ne kuma ba su san Harshen Larabci ba.
Sa’ad da yake ƙarami, iyayensa (Waɗanda Kiristoci ne) suka lura cewa yana iya karanta Alƙur’ani Shi Kaɗai duk da cewa babu wani Mahaluki da ya taɓa koya masa.
Yana da shekara Daya, Ya Daina shan nonon mahaifiyarsa.
Yana da shekara hudu ya fara karatun ayoyin kur'ani mai girma.
A lokacin yana dan shekara hudu ya iya karatun Al-Qur'ani gaba daya kuma ya na yin wa'azi cikin harsunan Larabci da Swahili da Faransanci ba tare da zuwa wata Makarantar ilimi Ba.
An ruwaito cewa maganarsa ta farko ita ce: “Ku tuba sai Allah ya yafe muku” kuma ya na fadar wadannan kalmomi da larabci. Iyayensa da suka damu, da farko sun ɗauka cewa aljanu ne, suka kama shi Sai suka kira fastoci don su yi masa addu’a.
Daga karshe dai makwabtansu musulmi ne suka fassara musu kalaman da Shariff yake Nufi, Bayan iyayensa sun gane muhimmancin abin da yaronsu yake faɗa da cewa Karama ce daga Allah, sai iyayensa suka musulunta.
Bugu da ƙari, duk da cewa ya fito daga Tanzaniya, yana magana da Larabci sosai ban da wasu harsuna 4 (Ingilishi, Faransanci, Italiyanci, da Swahili). Yana iya koyar harsuna da sauri, ya taɓa cewa: "Na je kasar Kongo na ji mutane suna magana da Lingala (Wani Harshe Ne A Kasar). Nan da nan na iya fara magana da Harshen.
Daya daga cikin kasashen da ya ziyarta domin gabatar da wa'azi ita ce kasar Gambia. Dubban jama'a ne suka yi dafifi a filin wasa na 'yancin kai, Wandanda da suka hada da manyan jami'an gwamnati da 'yan majalisar koli ta Musulunci domin sauraren wa'azinsa.
Yana gabatar da wa'azi da laccoci a Afirka da Turai wanda ya jawo dubban mutane ke sauraronsa. Saboda wannan yaron dubban mutane ne suka musulunta.
Daga baya yaron Sharif-uddin Daina yin Wa'azi bayan zargin da ake masa na cewa Lamarin Nasa wata zamba ce da aka shiryawa musulmin duniya baki daya.
Daga baya Sheriff-Uddin ya koma Kasar Gambia a 2007 don fara sabuwar rayuwa. Wani dan kasar Gambia ne da ya hadu da shi ta hanyar yanar gizo "ya dauki Dawainiyarsa bayan rasuwar iyayensa.
Yanzu Haka Sheik sheriffdeen yana da shekaru 30 a duniya “Yaro Mai Karama” dan Tanzaniya wanda ya musuluntar dubban Mutane yanzu Haka yana zaune a Gambia.