Akwai wasu nau’in abinci da ya kamata dan Adam ya dinga ta’ammali da su domin gujewa da kamuwa da wannan matsala da ta zama ruwan dare wato cutar hawan jini.
Bincike ya nuna cewa akwai wasu dangin abinci masu dauke da sinadarai dake taimakawa matuka wajen rage cutar hawan jini.
Masu bincike sun gano cewa kayan abincin suna cike da sinadari kamar Calcium, magnessium da potassium.
Ka hada su cikin nau’in kayan abinci da kake ci yau da kulum domin rage kamuwa da ciwon zuciya da bugun jini.
Ga nau’in abincin kamar haka;
1. Farin wake
2. Kayan abinci da aka sarrafa daga madara
3. kifi musamman Tilapia
4. Cakulati
5. Man zaitun
6. Ayaba
7. Inabi
Wadannan nau'in kayan abinci za su taimaka muku wajen kawar da ciwon hawan jini, da fatan za ku yi kokarin sanarwa da al'umma dake fama da wannan matsalar ta hawan jini.