Namijin Duniya: Wani Mutum Ya Kashe Zaki Bayan Sun Shafe Tsawon Minti 90 Suna kokawa



Wannan mutumi ya kashe zaki a gabashin Afirka, inda ya samu raunuka da dama bayan ya yi fada da zakin na tsawon mintuna 90 don kare iyalansa.


Hotunan dake da ban tsoro sun fito daga kasar Uganda bayan da rahotanni suka ce wani mutum ya kashe zaki da hannunsa a wasan kokawa da aka yi wanda yai sanadin zubar jini mai yawa daga jikin mutumin wanda za ku ga duk jikinsa daure da bandeji. 



Shafin Daily Star ta rawaito cewa mazauna yankin da mutumin ya fito sun tabbatar da faruwar al'amarin inda suka ce zakin ya yi kokarin shiga gidan mutumin inda suka fara yin kokawa da mutumin. 


An dauki hoton mutumin cike da raunuka a jikinsa duk an yi masa liki da bandeji kamar yadda kuke gani cikin wannan hoton wanda zai iya daukar tsawon lokaci kafin ya warke. 



Mutane da yawa ne ke ta cece-ku-ce a kan yadda mutumin ya nuna jarumtarsa su ka yi kokawa da zaki har ya kashe shi. 


Lamarin dai ya faru ne a gundumar Mpefu Kagadi na kasar Uganda. 


Shin za ku iya yin abinda wannan mutumin yai don kare iyalansa? Ku bayyana mana ra'ayoyin ku. 


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

31 Comments

  1. Gaskiya indani ne zan iya domain Kara iyalin na

    ReplyDelete
  2. Gaskiya na jinjina mishi. Nima dai abin da zanyi kenan saina ga abin da zai ture wa buzu nadi.

    ReplyDelete
  3. Masha Allah da Namiji kokari

    ReplyDelete
  4. Dakyau jarimi 👍👍👍👍

    ReplyDelete
  5. Allah sarki kauna iyaye Dan Allah kenan

    ReplyDelete
  6. Bazan iyaba 😂

    ReplyDelete
  7. Gaskiya wannan shine jarumi wallahi

    ReplyDelete
  8. ai Dama Rashin tsoro shine SOJA ba wai kakinba, lalle wannan agaishe shi namijin duniya Allah ya bashi lfy, Na bashi mukamin fild mashal.

    ReplyDelete
  9. 𝓜𝓪𝓼𝓱𝓪 𝓐𝓵𝓵𝓪𝓱 𝓝𝓐𝓜𝓘𝓙𝓘𝓝 𝓓𝓾𝓷𝓲𝔂𝓪

    ReplyDelete
  10. Allah yajinkanta saina auri wata😂😂

    ReplyDelete
  11. Ammafa ya cika namiji

    ReplyDelete
  12. Ina masu dawa to ga sarkin dawa.

    ReplyDelete
  13. Babu abinda zai ja man kokawa da zaki!

    ReplyDelete
  14. If I where you I will do the same

    ReplyDelete
  15. Kai nice man. Wish u quick recovery, an solute.

    ReplyDelete
  16. so mahaukace nee ldan ba so ba maixe kaika fada da xaki

    ReplyDelete
  17. Gaskiya yayi kokari, kuma haka akeson namiji.
    Koda ace nine, to wallahi zan iya yin haka.

    ReplyDelete
  18. Gaskiya Yayi kokari, kuma haka akeson namiji.
    Kuma koda acr nine haka zanyi.

    ReplyDelete
  19. Allah yakara karewa

    ReplyDelete
  20. Gaskiya ni akan iyalina Allah Zan iya sama da wannan saide ayi ragas

    ReplyDelete
  21. Tabdijam lallai yayi jarumta,amma nima zan iya kamantawa koda baikai kamar nasaba.hhhhhhh

    ReplyDelete
  22. abbam6413@gmail.com

    ReplyDelete
  23. Ai babu abinda namiji bazai iyaba wajen kare iyalansa

    ReplyDelete
Previous Post Next Post