Mura Tana Damuna Akai-akai, Menene Ke Kawo Hakan?




Tambayar da aka turo kenan wacce naga ya dace mu yi magana akai don mutane su karu.


Mura virus ke kawota shi kuwa virus yakan kama mutum ba tare da yasan ta ya hakan ta faru ba, sannan baijin magani sai dai idan yai sauki amma jiki ya kan taimaka wajen yakarsa ya hanashi tasiri.


Toh amma idan mutum na yawan mura wannan alamace ta yana da raunin sojojin jiki dake Kare jikinsa daga farmakin kwayoyin cuttuka (weak antibodies) wanda wannan rashin kuzarin sojojin kan iya zamowa sanadiyyar gado su daga mahaifa ko kuma dalilin wata matsala da mutum ke dashi.


Don haka kafin su sami kuzarin yakar kwayoyin cuta dole sukan bukaci sinadarin abinci mai gina jiki wato (protein) wannan sinadarin karancinsa nasa antibodies su yi rauni, haka jiki kan samar da wannan sinadarin yayin bacci kunga kenan ga wadanda basa samun isashshen bacci suma antibodies din su na raunana, don haka dole mutum ya rika samar wa jikinsa hutu, hasali mutum ma yafi kuzari yayin da yake cikin halin bacci.


Sauran abubuwan da za su taimaka shine mutum ya rika cin vegetables da fruits akai-akai (musamman lemon 6awo) hakan na kara gina garkuwar jiki tare da kauracewa shan magani daka, uwa uba daina raina cuta a jika da kinji canji Maza je kaga likita.


Sannan ake yawan yin wanka da ruwan dumi musamman lokacin murar. 


A duba fanka in ana amfani da ita a tabbatar ana kakkabe kurar jiki


A daina yawan tattaba hanci, baki zuwa kunne lokacin murar. 


A yawaita Shan ruwa tea mai citta sosai, shima zai taimaka, tare da Shan magani mai sinadarin Vitamin C


Wannan shine.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post