Kwanaki Kadan Kafin Sallah Magidanci Ya Koka Kan Mutuwar Ragonsa Da Zai Yi Layya.
Kwana 4 ne ya rage a yi babbar sallah inda Musulmi a fadin duniya ke jiran ranar domin yin layya. Sai dai wani magidanci ya koka kan mutuwar ragon da zai yanka jim kadan kafin sallah.
Magidancin ya wallafa labarin mutuwar ragon nasa a shafinsa na Twitter asafiyar ranar Asabar cikin jimami ya wayi gari ya tarar da ragon ya mutu.
Ga rubutun da ya wallafa Kamara haka;
"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un It's just a few days to sallah, And my sallah ram just passed away this morning. Allah yasa haka shine mafi Alkhairi. "
Bayan ya wallafa hoton ragon mutane da dama sun yi masa jaje tare da bashi hakuri kan abinda ya faru.