Ku Daina Wahalar Shan Magani Idan Namiji Ya Haura Shekara 20 Al'aurar sa Ta Gama Girma, Likita




Wani kwararren likita Dr Chinonso Egemba ya bayyana cewa duk namijin da yai shekara 21 alaurarsa ta gama girma duk irin maganin da zai sha ba za ta kara girma ba. 


Likitan ya bayyana hakan ne cikin wani faifan bidiyo da ya wallafa a shafinsa na Twitter. Likitan wanda yake yawan bayar da shawarwari ga ma'aurata ya yi Kira ga maza masu yawan shan magunguna don kara girman alaura su daina. 


A cewar sa Indai namiji yai shekara 21 ya gama girman azzakari babu wani magani na bature ko gargajiya da zai kara girmanta. 


Dr Chinoso ya yi kira da mazan da suka haura shekaru 21 da su yi hakuri da yanayin halittar azzakarinsu don gudun faruwar matsala. 

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post