Gyaran Jiki
Idan kuna son fata ta yi laushi da sheki ku samu wadannan abubuwan kamar haka:
Man zaitun
Lalle
Kur-kur
Madara
Zaki hade wadannan kayan hadin guri daya, sai ki kwaba su ki shafe jikinki da fuskarki, zakiyi wannan hadin kafin ki shiga wanka. Idan ya bushe a jikinki sai ki murje sannan sai ki wanke jikin, jikin yana yin kyau yayi sheki.
Gyaran Jiki 2
Wannan hadin shi ake cewa kafi TURGEWA, ku samu wannan abubuwan kamar haka;
kur-kur
dilka
zuma
kwai
lemun tsami
Ki hade su guri daya ki samu ki kwaba kamar yadda ake kwaba lalle, amma yafi kwabin lalle ruwa, sai ki shafe fuskarki. Idan kuma har da jiki kikeso, sai ki shafa harda jikin Bayan (1hr) sai ki shiga wanka zaki ga yadda jikinki zai goge.
Gyaran Jiki 3
Idan kuna son fata ta yi laushi da sheki, ku samu:
Lalle
Kwanduwar kwai guda 3
Manja cokali 3
kur-kur
Sai ki kwaba su guri daya ki shafe jikinki zuwa (1hr) daya, sai ki yi wanka da ruwan zalla da ruwan dumi ki shafe jikinki da ita sai ki kuma yin wanka.
Kyaun Fuska
Idan Kina Son fuska ta yi kyau ki samu wannan abubuwan Sai ki hade su guri daya ki kirba su cikin turmi, ki mulmula ki rinka wanke fuska zaki ga yadda fuskar ki zatayi
1.dettol
2.sabulun Ghana
3.garin zogale
4.farar albasa
Gyaran Fuska
Wanna hadin wanda ya kesa fuska tayi haske da annuri ta kore kurajen fuska, samu bawon kankana a rinka goge fuska da shi yana gyara fuska tayi sumul
Gyaran Fata
Ku samu wadannan abubuwan kamar haka;
1.Lemun tsami
2.bawon kwai
3.kur-kur
Zaki hade su guri daya ki daka su sai ki rinka wanka dashi fatar mace zata goge tayi kyawun gaske
Gyaran Fata
Ki samu wadannan abubuwan kamar haka;
1.ganye magarya
2. sabulun salo
Zaki daka ganyan magarya sai ki zuba a cikin sabulun salo ki rinka wanka dashi, yana gyara jiki
Gyaran Fata
Ganyan magarya
Man zaitun
Man habbatussauda
Ana daka ganyan magarya a zuba cikin man zaitun da man habbatussauda shi ma yana gyaran fata.
Gyaran Fata
Ki samu
lalle
garin ridi
Ana amfani da lalle kafin ki shiga wanka sai ki kwaba ki zuba garin ridi ki shafe jikinki zuwa (1) hr sai kiyi wanka.
Gyaran Gashi
Ki samu
Man zogale
Man kwakwa
Man zaitun
Zaki hade su guri daya ki rinka shafawa a kanki
Gyaran Gashi
Samu wadannan abubuwan kamar haka,
Man zogale
Ganyan magarya
Kanunfari
Sai ki hade su guri daya ki rinka shafawa a kanki yana sanya tsayin gashi ya kuma yi laushi
Gyaran Kafa
Baki ba zuwa wajen wanke kafa madarar kinyi amfani da wannan hadin, ki samu wannan abubuwan kamar haka
man shanu
man kwakwa
man ridi
man alayyadi
Idan kafa tana tsagewa ko tana kaushi da daddare zaki hada wadannan mayamayen guri daya ki shafa a kafa Idab zaki kwanta bacci daddare sai ki daure da Leda da safe ki wanke da ruwan dumi ki shafa man zaitun da man ridi
Maganin Ciwon Sanyi
Duk macen dake son ni'ima ta tabbatar mata, koda yaushe ta kasance cikin ni'ima to lallai ya zama dole ta magance matsalar ciwo sanyi
( Toilet Infection)
Domin magance wannan matsala ki samu wadannan kayan kamar haka;
hulba
bagaruwa
habbatussauda
Ki hada hulba da bagaruwa guri daya, ki dafa idan ruwan ya sha iska sai ki zauna a ciki, kuma ki samu man habbatussauda kiyi matsi dashi.