Ki sami ayarki ki tsinceta sannan ki wanke ki shanya, idan ta bushe sai ki zuba a turmi ki dakata lukwi, ki na dakawa kina tankadewa da rariya mai laushi.
Sanya amarya kuka
Sai ki daka dabinonki da cukwi da mazarkwaila ki daka su yi lukwi ki hada da dakakkiyar ayarki guri guda, ki sami mazubi na roba mai kyau mai murfi ki zuba, duk sanda zaki dinga sha sai kisa madara ko fresh milk ko danyen nono ko yoghurt me kyau, ba a bawa yaro mai kiwa.
Hadin Ni'ima 2
Ki samu wannan abubuwan kamar haka
aya
dabino
tafarnuwa
sugar da madara
Yadda Ake Yi
Zaki sami ayarki ki jika ta ta jiku sannan ki surfata, ki jika dabinon shi ma ya jiku sosai sai a markada da blander ko kuma a markado a inji amman kice sai an gama nikan gero sannan za'a nika miki don kada a nika a kan kayan miya don kada yayi yaji, sai ki zuba garin tafarnuwa a kai sai ki hada
da madara ko nono idan da hali a saka a firji yayi sanyi ko kuma a sanya kankara a kai a sha ba a bawa yaro.
Hadin Ni'ima 3
Ki samu wannan abubuwan kamar haka
gwanda
kankana
abarba
lemon zaki
kankara
sugar
Yadda Ake Yi
zaki sami gwandarki da kankanarki da abarba da ayaba ki yayyanka gwitsi-gwitsi kamar kan kuda inji yara- sai ki bare bayan lemon zaki ki shima har da wannan farar fatar ki cire kwallayen suma sauran ki ciccire kwallayen sai ki hada su guri daya ki kara ruwan kadan kisa sukari kadan idan kina da firji kisa a ciki idan kuma babu ki saka kankara akai ki ajiye shi narke sai ki tsiya ya ruwan zaki ga ya zama mai kauri kitib ki dinga sha zaki iya hadawa da yan gudaddajin ma.
Hadin Ni'ima 4
Ki samu wadannan abubuwan kamar haka;
dabino
madarar shanu
kanunfari gari
kirfa
Yadda Ake Yi
za'a sami dabino a shanya shi ya bushe sai a cire kwallon a dakashi lukwi, sannan a saka dakakkan garin kanunfari a hada a kurfa guri daya sai a dinga zuba cokali uku ana hadawa da madarar shanu ana sha safe da yamma cokali uku-uku kullum tsawon sati guda.
Hadin Ni'ima 5
garin idon zakara
garin tafarnuwa
ruwan khal
madarar shanu
Yadda Ake Yi
A sami garin idon zakara da garin Tafarnuwa a hada rabin cokali a zuba a kofi a zuba ruwan khal karamin cokali a hada da madarar shanu cikin kofi a hada a sha, akwai saukar da ni'ima.
Hadin Ni'ima 6
Samu wadannan abubuwan kamar haka;
ruwan rake
zuma
garin tafarnuwa
garin kanunfari
Yadda Ake Hadawa
A sami rake a nikashi a blander ko kuma a saka cikin tirmi mai kyau a daka a fitar da ruwan jiki, a zuba zuma mai kyau a kan ruwan raken a saka garin tafarnuwa kadan a zuba garin kanunfari rabin cokali a hada a dinga sha akwai saukar da ni'ima.
Ruwan Ni'ima 7
Ki samu
madarar shanu
ruwan khal
zuma
ruwan kankana
Yadda Ake Hadawa
A sami kankana a nikata ko a yankata gutsi-gutsi a zuba mata ruwa a barta ta
zagwanye a zuba a kofi a zuba ruwan khal da zuma a hada da madarar shanu a dinga sha shima yana da kyau.
Hadin Tukudi Na Gari
Ku samu wannan abubuwan kamar haka;
gero
kanunfari da citta da masoro
hakin daka
sassaken kankana
dabino
mazarkwaila
sassaken baure
Yadda Ake Yi
A sami gero a surfa shi a soya sam-sama sannan a dakashi ko kuma akai nika yayi laushi sai a zuba a tirmi a saka kanunfari garinsa da garin masoro da garin sassaken kankana da garin dabino da dakakkiyar mazarkwaila da sassaken baure a hadasu a daka su yilukwi a shanya su a faranti ya bushe sai a dinga sha madara ko nono ko yogot.