Cutar Ulcer shine samuwar kurji ko gyambo a cikin daya daga cikin bangarorin hanjin mutum. Sababin haka kuwa shine.
1 Damuwa irin ta rayuwa.
2 (Gastro intestine) wato yayin da sunadaran da suke diga a cikin hanji don narkewar abinci suka yi yawa, suna iya samar da Ulcer.
3 Amfani da tukwane ko kwanukan alminium wanda ake wanke su da soson karfe, wato birbishin aluminium din dake makalewa a jikin kwanon, shima yana kawo Ulcer.
4 Wani likita yana cewa, abinda ake kankarewa a jikin recherge card yana kawo Ulcer idan a ka ci abinci batare da an wanke hannuba.
5 Yawan amfani da abinci ko abin sha mai tsananin sanyi ko zafi.
6 Rashin tsabtace abinci ko abinsha, domin akwai wasu kwayoyin halittu kanana wanda suke iya rayuwa a jikin mutum kuma har suyi tasiri a hanjinsa.
Manzon ALLAH S.A.W yana cewa Tsabta tana cikin Imani!
Maganin Ulcer mafi shahara da tasiri da yaduwa a cikin littattfan likitancin musulunci suka ambata shine.
Ana hada Zuma (Honey) da garin Habbatus Saudah (Negela Sativa) da garin bawon Rumman (Pomgrenate) sai a hadasu a guri guda a rika shan cokali 2 sau 3 a kullum.
Idan Ulcer din takai nau'i na karshe daga nau'ukan Ulcer wato (Papetic Ulcer) ana gane wannan nau'i ne yayinda akayi gyatsa sai aji warin jini.
Itama insha Allah idan akai wannan maganin za'a samu waraka.
Allah yasa mu dace.