Akwai hanyoyin da dama da ake amfani dasu wajen mallakar mai-gida kamar haka:
1. ki iya kissar kwanciya, da nuna masa kauna a wajen kwanciya
2. ki so shi, ki so 'ya'yan sa da yan uwana gaba daya
3. Bari abinda bai so, da yin abinda yake so
4. ki kasance mai masa ladabi da biyayya da bin dokokin daya gindaya miki
5. tarairayarsa da tarba mai kyau a duk lokacin da ya shigo gida
6. tsaftar jiki iya girki, da kula da tarbiyya yara
7. tausayinsa akan al'amuran da kuma idan yana cikin wani hali
8. son ibada, imani da kyautatawa ga danginsa
Tunatarwa
Babu wani Wanda zai iya juyo miki da hankalin mijinki, da ya wuce ke, saboda haka muddin kika rike wadannan sai kin yi masa mallakar da ba macen da zata iya juya shi sai ke.
Shawara Ga Mata Masu Aiki;
Don Allah 'yan'uwa mata mu dinga kokari muna kare mutuncinmu da na mazajenmu a wurin da muke aiki, musamman masu aiki a (local government da state) saboda sai kaga matar aure ba ta da kawa a wurin aiki mace, duk abokanta maza ne.
To ko baki da aure, ai bai kamata a matsayinki na mace mai rauni, balle kina da aure ace kina abota da maza. Idan kina wannan kullum mutuncin ki raguwa zai yi ba karuwa ba, kuma sai Allah ya kamaki ko kuma ya kama mijinki ranar gobe kiyama, kin ja masa kenan, tunda shi da ya bar ki zuwa aiki, bai yi tunanin haka Zaki yi ba.
Mu dinga kulawa da irin wannan, saboda sai kaga mace cikin kankanin lokacin tana abokai maza da yawa kuma ko ba kya fasikanci wannan fuskar da kika bayar, shi zai sa kare da biri kowa ya nemeki da fasikanci, saboda kin saki kanki kin zama kamar haja a Kasuwanci, ki zauna kina Hira da su barkatai, ki na sakin zance da bai dace ba har tafi da shewa, Allah ya ganar damu.