Wasu daga cikin maza a tsorace su ke dangane da wannan zato game da wannan nagarta, mata su na da mabambantan ra’ayoyi akan batun. Gaskiyar batun za ta iya ba ku mamaki.
Tare da rayuwar maza akan shekarun tsufa, shin gaske ne girman Azzakari shi ne abin duba dangane da jima’i ? Wannan tambayar ta na jefa damuwa da tsoro a zukata, maza su kan yi la’aakari da cewa ba su da nagarta a fannin.
Amsar tambayar ta na da ruɗani fiye da yadda ku ke tunani. Sannan kuma abin takaici, matsalar ta fi zama matsala ta kaitsaye akan nazarinka fiye da na abokiyar rayuwar ka.
Girman Azzakari: Gaskiyar Al’amari Da Saɓanin Fahimta:
A haƙiƙanin gaskiya tunda farko, a cewar binciken ilimi na mujallar nazariyyar halayyar maza da ƙarfin Azzakari, yanayin girman Azzakari na mafi yawan maza kaso 68 ya na tsakanin girman inci huɗu da ɗigo biyar, (4.6 Inches Long).
A game da kaso 16 kuwa girman nasu azzakarin ya na tsakanin inci shida da ɗigo ɗaya, (6.1 Inches). Sannan kuma akwai kaso 2.5 waɗanda girman nasu ya ke inci 6.9). Game da kaso 16 na maza su na da girman azzakari da inci 4.5, tare da kaso 2.5 waɗanda nasu ya ke ƙasa da girma inji 3.7.
Saboda haka yanzu ka san wannan. Amma ka san waye ya damu game da girman azzakari ?, Duba Wannan Batu:
A dai cikin wancan bincike sama da mutum 52,000 da su ka taka rawa, maza da mata, kaso 45 na maza sun ba da rahoton cewa ba sa gamsuwa da girman Azzakarinsu na buƙatar ya zama babba. A haɗa da kaso 16 waɗanda su ke da ƙanƙantar azzakari ƙasa da matsakaici. Sannan kuma hasashen bai sauya ba game da sauyin shekaru ba. Ko dai akan adadin lambar maza tsofi inda su ke da damuwa da ƙanƙantar Azzakari da kuma matasa.
Waɗannan duba akan rashin nagarta su na da sakamakon damuwa. Mazan da su ka yi imani cewa azzakarinsu ƙarami ne sosai ba su cika damuwa da nuna gwanintarsu a gaban abokiyar rayuwarsu ba. Sun fi buƙatar ɓoye azzakarinsu a lokacin jima’i. Sannan sun fi sha’awar su yankewa kansu hukunci rashin sha’awa.
A ɗaya ɓangaren kuma mazan da su ke jin cewa su na da babban Azzakari sun fi sha’awar sun nuna ƙwarin gwiwarsu da imani da kansu game da jawo hankalin saduwa. Abin sha’awa kaso 84 na mata binciken ya tabbatar da cewa sun bayyana gamsuwarsu da yanayin girman azzakarin abokin sadauwarsu a lokacin jima’i. Saboda haka ba matsalarsu ba ce.
Yanayin girman azzakari ba shi ne abin duba ba a gun mata, amma idan mata su na magana akan girman azzakari su na magana ne akan yanayin kauri da ƙarfinsa ba wai tsayi ba.
“Tun daɗewa, fatar azzakari ba ita ce jin daɗi ba a matsayin gajera, ƙaton Azzakari ga mafi yawan mata”, cewar Patti Britton, Phd, mai ba horon ilimin jima’i, kuma ƙwararriyar masaniyar ilimin jima’i a Los Angeles, Calif. “Ba shakka jinyar azzakarin namiji shi ne ginshiƙin da ya ba ta damar jin abin da mu ke ciki akan ilimin jima’i da ake kira da gamsuwa. Jin gamsuwa cikakkiya ta na samuwa ne daga Azzakari da kuma lafiyayyen farji”.
Girman Azzakari ba wai shi ne dalilin abu na ƙarshe da ke bayyana damar ɗa namiji ke da ita ta gamsar da mace ko jindaɗin jima’i ba.
Wurare biyu masu saurin gamsar da mata saduwar jima’i su ne cikin ɓelinta da gefe, Britton ta yi bayanin cewa “ga matan da su ke da ƙwarewa a wannan fanni, duk Azzakarin da ya shige su ƙarami ko babba zai gamsar da su”.
“Bayani na gaskiya shi ne, lamarin ba wai a girma ya ke ba, idan har namiji ya na da ƙwarewa da dabarun soyayya ta kowane fanni, zai yi nasara ya samar da jin daɗi da gamsuwa matuƙa a lokacin da ya ke jima’i”. Inji Brittoñ.