Bayani Akan Layya Da Hukunce-Hukuncenta A Musulunci - Android Pols



Layyaha harshen larabci- Shi ne: Yanka abun layya a lokacin walaha. A shari'ar Musulunci kuma Itace: Abun da ake yankawa na Rakuma da Shanu, Awaki da Tumaki, don neman kusantar Allah madaukakin sarki a ranar idi.


Hukuncin layyah da kuma dalilan shar'antata: Hukuncinta sunna ne mai karfi; saboda fadinsa madaukakin sarki:


ﭽ ﮊ ﮋ ﮌ   ﭼ الكوثر: ٢

Ma'ana: (Ka yi sallah ga Ubangijinka, ka kuma soke Rakumi ga Ubangiji) [Kausar: 2]. 


Da kuma saboda hadisin Anas (RA)


"أنَّ النَّبِيّ r ضَحَّى بِكَبْشَيْنِ أَمْلَحَيْنِ أَقْـرَنَيْنِ، ذَبَـحَـهُمَا بِـيَدِهِ، وَسَـمَّى وَكَـبَّـرَ، وَوَضَعَ رِجْلَهُ

عَلَى صِفَاحِهِمَا"([1]).


Ma'ana: (Lallai Annabi SAW ya yi layyah da raguna guda biyu masu rodin fari da baki, madaidaita kaho guda biyu, ya yanka su da hannayensa, yana mai Ambaton sunan Allah, da yin kabbara, ya kuma dora kafarsa a gefen wuyansu).


Abin da ake cewa Layya shi ne duk wata halastacciyar dabba da aka yanka domin neman kusanci ga Allah.


Layya tana da asali a cikin Kur’ani da Hadisin Annabi (SAWW). A cikin Kur’ani Allah (TWT) Yana cewa: “Ka yi Sallah ga Ubangijinka kuma ka yi yanka.” (Kausar: 2).


A Hadisi kuwa Anas bin Malik (RA) ya ruwaito cewa: “Manzon Allah (SAW) ya yi layya da raguna biyu bakake, masu kahonni.


Ya yanka su da hannunsa, ya yi bisimillah ya yi kabbara, ya kwantar da su ta gefen wuyansu” (Muslim ya ruwaito).


Akwai Hadisai masu yawa a kan layya inda a shekara ta biyu Bayan Hijirar Annabi (SAW) aka shar’anta yin layya.


Ita layya Sunna ce mai karfi, tana hawa kan wanda ya cika sharudda masu zuwa:


1. Ya kasance da ba bawa ba, a nan ba batun namiji ko mace. Tana zama Sunna a kan mutum ga kansa da iyayensa, idan talakawa ne da ’ya’yansa maza idan ba su balaga ba da ’ya’yansa mata idan ba su yi aure ba.


Ba Sunna ba ce a kan mutum ya yanka wa matarsa ko dansa da aka haifa a Ranar Layyar.


2. Kada ya kasance mahajjaci, domin shi mahajjaci, hadaya ce a kansa.


3. Ya zama ba matalauci ne ba. Ma’ana kada ya zama yana bukatar kudin yin Layyar domin biyan wasu bukatu nasa.


Amma idan zai iya cin bashi ya yi Layyar, to ya yi, idan ya san zai iya biya, ba tare da takura ba. Wadansu malaman sun ce kada mutum ya ci ba shi domin ya yi Layya.


Dabbobin da ake yin Layya da su Dabbobin da ake yin layya da su kadai su ne: Rakumi da sa da rago da taure da matansu.


Rago sai wanda ya shekara, taure kuwa sai ya shiga shekara ta biyu. Sa kuma sai wanda ya kai shekara uku. Shi kuwa rakumi sai ya kai shekara biyar.


A wajen Layya, rago ya fi falala (sai tunkiya), sai taure (sai akuya), sai kuma sa (sai saniya). Bayan sa sai kuma rakumi (sai taguwa).


A cikin kuma dukkan dabbobin da aka ambata an fi fifita mazansu a kan matansu, lafiyayyunsu (wadanda suke iya yin barbara) kuma a kan fidiyayyunsu (wadanda ba sa iya yin Barbara saboda an dandake su).


Sai dai idan fidiyayyun sun fi kitse ne sai a yi da su.


Kubutuwa daga Nakasa 


An shardanta ga rakumai da shanu, awaki da tumakin da za yi layyah da su; cewa su kasance sun kubuta daga Nakasa da za su sanya naman dabbobin ya karanta; don haka;


Yankwananniyar dabba ba ta isarwa, haka kuma karyayyiya, da mai ido daya, da maras lafiya; wadannan kuma saboda hadisin Al-bara'u dan Aazibin (RA) daga Annabi (SAWW) ya ce:


"أَرْبَعٌ لا تُجْزِئُ فِي الأَضَاحِيِّ: الْعَوْرَاءُ الْبَيِّنُ عَوَرُهَا، وَالْمَرِيضَةُ، الْبَيِّنُ مَرَضُهَا، وَالْعَرْجَاءُ الْبَيِّنُ عَرَجُهَا، وَالْعَجْفَاء الَّتِي لا تُنْقِي"([7]).


Ma'ana: (Dabbobi guda hudu basa isarwa a "layyah": Dabba mai harara-garke wacce matsalan idonta ya bayyana, da maras lafiyan da cutarta ta bayyana, da gurguwar da gurguntakanta ya bayyana, da kuma ramammiyar da bata da kitse).


Kuma ana "qiyasi" ga wadannan Nakasa guda hudu, duk wani aibin da ke da irin ma'anarsu; kamar dabbar da hakoranta na gaba suka fadi, da wacce mafi yawan kunnenta ko kahonta ya yanke, da makamancin haka na daga Nakasa. 


MLokacin yanka abun layyah:


Lokacin yanka layyah na farawa ne daga bayan sallar idi ga mutumin da ya sallace ta, ga mutumin da bai sallace ta ba kuma (saboda uzuri): bayan fudowar rana na yinin idi da gwargwadon lokacin da za a iya yin raka'oi guda biyu, da hudubobi biyu; wannan kuma saboda hadisin Al-bara'u dan Aazib (RA)yace: Manzon Allah (SAWW) ya ce:


"مَنْ صَلَّى صَلاَتَنَا، وَنَسَكَ نُسْكَنَا فَقَدْ أَصَابَ النُّسُكَ، وَمَنْ ذَبَح قَبْلَ أَنْ يُصَلِّيَ فَلْيُعِدْ مَكَانَهَا أُخْرَى"([8]).


Ma'ana: (Duk wanda ya yi sallah irin tamu, ya kuma yi yanka irin namu to lallai ya dace da yankan layyah akan tafarki, Amma mutumin da ya yi yanka kuma gabanin ya yi sallar idi to sai ya sake yanka wata a madadinta). Lokacin yankan dabbobin na cigaba har zuwa faduwar ranar yinin karshe daga cikin kwanakin "attashriq" (wato: 13/ ga watan: 12); saboda hadisin Jubair dan Mudim daga Annabi (SAWW) yace:

"كُلُّ أَيَّامِ التَّشْرِيقِ ذَبْح"([9]).


Ma'ana: (Dukkanin ranakun "tashriq" lokacin yanka ne).


Abin da ya fi falala shine a yanka abun laiyan bayan an idar da sallar idi; saboda hadisin Al-bara'u dan Aazib (RA) lallai Annabi (SAWW) yace:


"أَوَّل مَا نَبْدَأُ بِهِ يَوْمنَا هَذَا نُصَلِّي، ثُمَّ نَرْجِعُ فَنَنْحَرُ، فَمَنْ فَعَلَ ذَلِكَ فَقَدْ أَصَابَ سُنَّتَنَا، وَمَنْ ذَبَحَ قَبْلَ ذَلِك فَإِنَّمَا هُوَ لَحْمٌ قَدَّمَهُ لأَهْلِهِ؛ لَيْسَ مِنَ النُّسُكِ فِي شَيْءٍ"([10]).


Ma'ana: (Abun da zamu fara yininmu wannan da shi, shine mu yi sallar idi, sa'annan sai mu dawo don mu soke abun layyarmu. Duk wanda ya aikata haka to ya dace da sunnarmu, Duk kuma mutumin da ya yanka abun layyansa gabanin haka to ya sani cewa: nama ne ya gabatar da shi ga iyalansa, ba layyah ba).


Bayanin Dai Takaitacce ne

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post