Bambanci Tsakanin Maniyyi, Maziyyi Da Wadiyyi - Android Pols




Akwai sakonni da dama daga 'Yan uwa da suka yi tambaya (wata tambayarma tafi wata guda) akan banbancin wadannan ruwaye.


Hakan yanuna kishinsu ga addini wanda yasa mukayi tunanin sanyawa a fili wadanda basu tambaya bama su amfana.


Nadade ina tunanin sawa dan sauwakewa kaina amsa tambayoyi daya bayan daya.


Amma inajin Nauyi wajen bada amsa yasa nakasa, yauda aka kuma yi mini tambayar naga yadace in sanya tunda. "innalaaha la yastahyi minal haq.


Nana A'isha tana cewa:

"Allah ya jikan MATAN MADINA ko kadan Kunya bai taba hanasu neman sanin addininsu ba"


Idan mukace za muci gaba da jin nauyin tambaya ko bada amsawa saboda KUNYA to zamu rayu cikin jahilci, wanda wannan ba uzuri bane a wurin Allah.


Dan haka ga banbancin dake tsakaninsu:

1. Maniyyi


Maniyyin namiji:

ruwane mai kauri FARI wanda yake fitowa yayin babbar sha'awa kamar saduwa, ko wasa da farji.


Sannan yana tunkudo juna lokacin da yake fitowa, kuma warinsa yana kama da warin hudar dabino, ko damammen gari, Idan yabushe yana kamshin kwai.


1A. Maniyyin Mace:

Ruwane tsinkakke, mai fatsi-fatsi, wani lokacin kuma yana zuwa Fari, wanda yake fitowa yayin babbar sha'awa kamar saduwa, ko wasa da farji.


Sannan yana tunkudo juna lokacin da yake fitowa, za ta ji tsananin sha'awa da dadi lokacin fitowarsa. Kuma warinsa yana kama da warin hudar dabino ko damammen gari, Idan ya bushe shima yana kamshin kwai.

Sannan sha'awarta zata yanke bayan fitowarsa.


Hukuncin Fitar Maniyyi shine: Yana Wajabta Wanka.


2. Maziyyi 


Ruwane tsinkakke da yake fitowa, yayin karamar sha'awa, kamar tunanin aure ko kuma tuna wacce kakeso, ko matarka, ko kallon matar ko namijin da kike sha'awa.


Haka kuma yana fitowa yayin wasa tsakanin miji da mata, sai dai shi baya tafiyar da sha'awa, kuma wani lokacin ba'a sanin yafito.


Malamai suna cewa:

Maziyyi yafi fitowa mata, fiye da maza.


hukuncin sa Shine :

A Wanke farji Gaba Daya, Da Kuma Inda ya Shafa, Kuma a Sake alwala.


3. Wadiyyi 


Wani ruwane mai Kauri da yake fitowa a karshen fitsari, ko kuma karshen bahaya ga wanda ya jima baiyi jima'i ba, yana fitowa ga wadanda basuda aure, ko wadanda sukayi nisa da abokin rayuwarsu ta aure, ina nufin namiji ko mace.


Yana Daukar hukunce-hukuncen Fitsari, Allah shine mafi sani.


Nan gaba kadan zan kuma bayani a kan yadda ake wankan haila da na janaba idan Allah yaso kuma ya yarda.


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post