Ana bukatar mutum ya dinga shan ruwa akai akai, domin masana kiwon lafiya sun bayyana cewa shan ruwa akai-akai na yaki da cututtuka da dama.
Musamman shan ruwa da safe kafin aci komai na da fa'ida kamar haka:
1- Shan ruwa da sassafe na samarwa da jikin dan Adam karin ruwa, duba da irin sa’o’in da aka dauka ana bacci.
2- Shan ruwa kafin a ci abinci da safe na kara karsashi da karfin jiki.
3- Shan ruwa da sassafe kafin a ci komai na tada kwakwalwa.
4- Shan ruwa da sassafe kafin a ci komai na tsaftace jiki daga cutuka.
5- Shan ruwa da sassafe kafin a ci abinci na yakar cutuka tare da kara garkuwa ga jikin dan Adam.
6- Shan ruwa da sassafe yana sa narkewar abinci kamar yadda ya dace.
7- Hakazalika, yana sa a rage kiba, ga masu muguwar kiba.
8- Yana gyara launin fata tare da sanya walwalin fata da walkiya.
9- Yana kariya daga ciwon koda tare da tsaftace mafitsara daga kwayoyin cuta.
10- Shan ruwa da safe kafin cin abinci na taimakawa tsawon gashin kai tare da walkiyarshi.