Alheran Dake Cikin Kwanaki 10 Na Watan Zul-Hajji - Android Pols

 

Watan Zhul Hijjah shi ne wata na 12 a kalandar Musulunci, kuma a cikinsa ne ake gudanar da aikin hajji wanda yana cikin shika-shikan musulunci guda biyar da ake so ko wanne musulmi ya yi idan ya samu iko.


A Cikin Watan falalar Watan Zul-Hajji akwai aikin Hajji akwai Arafa. Dalili kuwa Allah Yana cewa a cikin Suratul Hajji aya ta 27-28 da kuma Suratul Bakara aya ta 198.


Suratul Hajji Aya ta 27 da 28: “Kuma ka yi shela a cikin mutane saboda yin Hajji, za so zo maka matafiya a kasa da kuma kan kowanne rakumi za su zo maka daga kowane lungu mai nisa Don su halarci amfanin da za su samu kuma su ambaci sunan Allah cikin kwanaki sanannu a kan abin da Muka arzuta su da shi na dabbobin ni’ima (wato rakuma da tumaki da shanu ), sai ku ci daga gare su kuma ku ciyar da galabaitaccen matalauci.”


akwai aikin Hajji akwai Arafa. Dalili kuwa Allah Yana cewa a cikin Suratul Hajji aya ta 27-28 da kuma Suratul Bakara aya ta 198.


Suratul Bakara Aya ta 198: “Babu laifi a kanku ku nemi falala daga Ubangijinku (wato ku nemi arziki ta hanya saye da sayarwa) idan kuwa kuka koma daga Arafa sai ku yi ta ambaton Allah a daidai Masha’aril-Haram (ta yin hailala da kabbara da hamdala), ku tuna Shi kamar yadda Ya shiryar da ku (ga ayyukan hajjinku da sauran ayyakan addininku) koda yake ku kasance da can kafin (shiriyar) cikin batattu.”


Goma na Farko ga Zul-Hajji, ayoyi da yawa sun yi magana a kansu (Allah Yana cewa a cikin  Suratul Hajji Aya ta (28):


“(28) Don su halarci amfanin da za su samu kuma su ambaci sunan Allah cikin kwanaki sannanu a kan abin da Muka arzuta su da shi na dabbobin ni’ima ( wato rakuma da tumaki da shanu), sai ku ci daga gare su kuma ku ciyar da galabaitaccen matalauci.” Kwanakin nan su ne kwana 10 ga watan Zul-Hajji, don Allah Yana cewa a cikin Suratul Fajari, Aya ta 1-2:


(1) Ina rantsuwa da alfijir


(2) Da darare goma.”


Darare goman nan su ne ake nufi da kwanaki goma na watan Zul-Hajji kuma kuma kamar yadda ayoyi sun tabbatar da muhimmancin  wadannan kwanaki haka Sunnah ta tabbatar da falalarsu. 


An samo Hadisi daga Dan Umar (RA), ya ce “Manzon Allah (SAW) ya ce, “Babu wata rana da ta fi girma a wajen Allah kuma Ya fi so kuma aiki mai kyau ya fi lada a cikinsu kamar kwanaki goma na Zul-Hajj. (Don haka ne Annabi ya ce) ku yawaita fadin la’ilaha illallah wal hamdulilah wallahu akbar.” Imam Dabarani da Baihaki suka fitar da Hadisi.


Daga cikin falalar kwanaki goma na farkon wannan wata, malamai sun ce an samu Hadisi daga Manzon Allah SAW da yake cewa: "Babu wani aiki a wajen ALlah SWT da yake da matukar lada kamar aikin da bawa zai yi a kwanakin 10 na farkon Zul Hijja. Sai Sahabbai suka tambaye shi, 'Ko da kuwa jihadi ne saboda Allah?' Manzo SAW ya amsa da cewa, "Ko da kuwa jihadi ne saboda, sai dai idan mutum ya fita jihadin da dukkan dukiyarsa ya kuma koma gida ba tare da komai ba." Bukhari ne ya ruwaito.


Malamai da dama sun ce kamar yadda kwanaki 10 na karshen watan Ramadan ke da falala, haka ma kwanaki 10 na farkon Zul Hijjah ke da falala.


Daga cikin falalarsu kuwa akwai ayyukan da ake so bawa ya dukufa yi na ibada don neman yardar Allah.


1. Daga cikin falalar kwanaki 10 na farkon watan Zul Hijjah akwai yin aikin Hajji'


Aikin Hajji daya ne daga cikin shika-shikan musulunci guda 5, da Allah SWA ya umarci dukkan musulmai gudanar da shi akalla sau daya a rayuwarsa.


Aikin Hajji ya wajaba akan wanda ya ke da lafiyar jiki, da lafiyar yin tafiyar, da kuma abin da zai yi guzuri da shi, tun daga yin tafiya zuwa kasa mai tsarki (makka) daga duk inda ya ke a duniya.


2. Ana so mutum ya yi azumi a kwanaki taran farko na watan, musamman ma na ranar Arafah. Azumin Arfah yana da falala sosai amma ba farilla ba ne, amma Ubangiji ya yi alkawarin gafartawa wanda ya azumci yinin.


3. Ana so a yawaita zikiri da kabbara a wadannan ranaku 10 na farkon watan Zul Hijjah.


4. A yawaita yin sallar dare


5. Ana so bawa ya yawaita tuba da neman gafarar Ubangijinsa.


6. Ana so mutum ya yawaita karatun Al-qur'ani.


7. Ana so mutum ya kara kaimi wajen yin kyawawan ayyuka kamar sadaka da taimako da sauransu.


8. Yin layya a ranar goma ga watan Zul Hijjah ga wanda yake da halin abin yankawa.


9. Halartar sallar Idi.


10. Yawaita yin godiya ga Allah Subhanahu wa ta'ala.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post