Wasu saboda sun rabu da mazansu ne. Wasu mazan basa tare dasu. Wasu matan kuma haka nan kawai mazan suke daina saduwa dasu ko kuma su da kansu su nuna basu da sha'awar Jima'i da mazajensu. Ko ma dai menene dalilin dake hana ki Samun biyan bukata irin na Jima'i, Kina da nakasu saboda rashin yinsa ga lafiyar ki.
Da zaran mace ta daina samun Jima'i kamar yadda ya kamata za a sameta da yawan fushi, da kuma kasala. Haka nan kawai abu zai rika bata mata rai ba tare da wani dalilin ba. Sannan a ko da yaushe jikinta babu karfi.
Baya ga hakan masanan sun tabbatar da cewa rashin samun yin Jima'i ga mata yakan sa su saurin mantuwa da kuma disashen kwakwaluwa.
Tunani da hankalin macen da take yin Jima'i yafi na wacce bata samu.
Matan da basa samun gudanar da Jima'i akai-akai a yawancin lokuta suna cikin cuta. Ciwo mai sauki irin mura idan ya kama macen da bata samun sabis sai ya jima bai warke ba. Amma macen da take samu nan take yake bacewa.
Kamuwa da cutuka cikin sauki yafi addabar macen da bata Jima'i. Farjin macen da bata samun Jima'i zai tsuke, kofar gabanta zai dawo karami, yadda duk lokacin da za a sadu da ita sai taji ciwo.
Haka nan macen da ba a yawan saduwa da ita tana iya fuskantar bushewar farjinta ko kuma zuban ruwa a gabanta a wasu lokutan.
Sannan duk lokacin da zata yi al'ada sai ya zo mata da zafi da kuma ciwo ba kamar macen da take samu ba.
Idan mace ta dauki tsawon lokaci babu Jima'i takan iya daina jin sha'awar Jima'i a tare da ita zata ji sha'awa ya dauke mata. Duk wannan illar rashin sabis ke kawosu.
Cardiovascular wani cuta ne inji masana dake iya kama duk wata mace da ta jima bata hau network ba ma'ana ba ta yi Jima'i ba. Sukace shi yawan saduwa ga diya mace yakan taimakamata wajen kubuta daga kamuwa da cutar da zuciya.
Yanzu dai Maza da Mata kunji illar da rashin Jima'i ke iya jawowa Dan Adam ga lafiyarsa. Da fatan za a bi hanyoyi na halak wajen yin Jima'in akai-akai.