Yadda Mace Za Ta Samu Karbuwa Wajen Uwar Mijinta - Android Pols




Iyaye sunada matukar tasiri a zamantakewar aure da 'ya'yansu a kowani hali da kuma yanayi.


Don haka ne a zamanin baya iyaye ne ke zabawa 'ya'yansu maza ko mata wadanda za su aura, hakan kuma yayi matukar tasiri a wannan lokacin ganin yadda ake samun aure na mutu karraba sabanin abubuwan da suke faruwa a yanzu. Duk kuwa da wasu gidajen har yanzu iyaye ke da alhakin nemawa 'ya'yansu wadanda za su aura.


Rashin jituwa ko fahimta da ake samu a tsakanin iyayen miji da matarsa ya fi yawaita a tsakanin uwar miji, domin yana da matukar wuya kiga cewa uban miji ne ya takura matar dansa ko kuma basa zaman lafiya da juna. Wannan dabi'ar da ko nace al'ada yafi yawaita ne a tsakanin uwar miji da kuma matar danta, wanda wasu da dama na mamakin abubuwan dake haddasa irin wannan matsalar.


Ga duk wata matar da ta ke son more zaman aurenta, ya zamemata wajibi ta sha maganin zama da uwar mijinta ko da kuwa ba a gida daya suke ba ko kuma gari guda kai koma kasashen da suke zaune ya babbanta.


Muddin uwar miji ba ta yi dake, to ko bongon duniyan nan kika tafi da mijinki kuka zauna don gudun matsala ko tashin hankali, to kinyi a banza muddin dai suna haduwa da danta ko tana magana dashi. Don haka abun yi kawai shine duk irin son da ta ke miki kafin aure, to ki tabbata kin kara samu wasu dabarun iya zama da ita.


Kuskuren da akasarin mata suke yi shine, na rashin yiwa uwar miji ladabi da biyayya don wai tana tunanin cewa mijinta yana sonta.


Babu dan kwarai da zai bari matarsa ta wulakanta masa uwa don dai yana sonta. Dole ne duk darajar ki ko na gidanku ki nunawa uwar mijinki ladabi da biyayya fiye ma da iyayen da suka haifiki domin ke dolen iyayenki ne amma ba dolen uwar mijinki bace.


Komin tsufanta, komin talaucinta ya zama babu raini ko tsana tskanin ke da ita, koda kuwa a zahiri bata sonki, ki ci gaba da yi mata biyayya wataran dole ta saduda.


Wani abun kula kuwa shi ne, kada ki sake ki aure namijin da kika tabbatar da cewa uwarsa bata kaunarki komin son da kike yi masa ko kukewa juna ki hakura, idan kuwa kika ki auren bazai jima ba kina iya zama bazawara.


Ki nemi amincewar uwar mijinki ta hanyar gamsuwa da cewa tabbas tana wa danta sha'awar ya zauna dake a matsyin matarsa, muddin hakan ya samu matsalar da za ta taso mai sauki ce.


Ko wace uwa tana son mai son danta, don haka ki nunawa uwar mijin ki kai tsaye ko a kaikace cewa kina fa son mijin nan naki. Ta hanyar nuna damuwa a lokacin bakin ciki ko wani bacin rai ya faru, haka kuma nuna murna da farin ciki idan abun alheri ya sameshi.


Kuma kada ki boye mata wajen kokarin da kike yi wajen kula da dukiyoyinsa da ya bari a karkashin kulawarki, kuma kada ki nuna kyashi ga kyauta da zai yiwa 'yan uawansa a gaban mahaifiyarsa.


Duk wata uwa baya ga son da ta ke yiwa 'ya'yanta, sai kuma jikokinta. Ki kasance mai kula da 'ya'yanki sosai da sosai, kuma ki kula cikinsu wanda uwar mijinki taso kema ki daukakeshi. Kada ki furta wata bakar magana ko dukan 'ya'yanki a gaban uwar mijinki kuma kada ki bari suna aikata wani mugun abu a gabanta baki hanasu ba.


Kamar yadda kowace mace take kishin mijinta, haka uwar miji take kishin danta. Kada ki sake ki nunawa uwar mijinki ai kece da gidan sai yadda kike so za ayi, idan kika bari uwar mijinki ta fahimci hakan, dake da ita babu sauran zaman lafiya kuma. Domin uwa gani take itace ta dace da ta juya danta amma ba wata mace ba.


Ki yawaita yiwa uwar mijinki kyauta musamman na abunda kikasan tana sha'awa na cine ko kuma na sanyawa a jiki. Ya zamanto lokaci - lokaci kina samun wani kyauta na musamman kina yi mata.


Uwayen maza suna son matan 'ya'yansu suna shawara dasu mussamman akan abunda ya shafi jikokinsu ko kuma wata shawarar na alheri da ta ke so a baiwa mijinta ko da kuwa ita da kanta tana iya bashi, yana da kyau ta soma tattaunashi da uwar mijinta domin ta fahimtar da ita cewa itama a kullum burinta shine ci gaban mijinta.


Idan kina da hali, ki rika daukar surukar ki kuna fita ziyarar 'yan uwanki ko nata tare, idan ya kama ma ki dauketa da jikokinta idan akwai ku fita yawon shakatawa domin debe mata kewa, a kuma kaita wuraren bada sha'awa da zata so.


Ki kula da al'adunta ko addininta domin ki girmamasu. Yana iya yiwuwa al'adunki dana surukarki daban, haka kuma addininku shima daban, to kada ki kyamaceta domin hakan, abunda kikaga sunayi ana al'adunsu ko addinsu wanda bai saba da naki ba kema kiyi, wanda kuma ya ci karo da naki cikin hikima da dabara sai ki nuna musu rashin amincewarki dasu.


Kada ki sake ki bari ko da wasa ku rika zagin wani ko wata da uwar mijinki, haka kuma kada ki amince da duk wata shawarar da zata zo miki da ita wacce bata da kyau, kamar zuwa wajen bokaye da 'yan bori domin neman wata biyan bukata. Ko kuma zagin kishiyoyinki, kiyi kokari kaucewa duk wata bakar al'adar da zata yi kokarin cusaki ciki yin hakan zai yi miki tasiri nan gaba, domin ko wani ne yace mata kinyi makamancin hakan zata miki kyankayawar shedan. Kiyi zaman aure domin Allah.


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post