Abd Allāh bn Umar bn al-Khaṭṭāb sahabi ne ga annabi Muhammad SAW kuma ɗan halifa Sayyadina Umar ( RA) na biyu. Ya kasance fitaccan Masanin hadisi da shari'a. Ya kasance tsaka tsaki a lokacin waki'ar Fitina ta farko.
An haifi Abd-Allah bn Umar Dan Umar bn al-Khattab A Sgekara ta 614. Sunan mahaifiyarsa Zainab bint Mazaun Jamiah.
Kafin Musuluntarsa Sayyadina Umar ( RA) yana da mata uku, duk da haka, bayan ya musulunta sai kawai Zainab ta bi mijinta wajen karbar addinin Musulunci, Shi ma Abdullahi ya karbi Musulunci tun yana karami, amma ba a bar shi ya shiga yakin Annabi Muhammad (Sallallahu Alaihi Wasallam) ba har sai da ya kai shekara sha biyar. Yakin farko da ya yi a kai shi ne da dakarun Abu Sufyan a lokacin yakin ( Gwalalo,) wanda ya faru a shekara ta 627.
An karbo daga Salim bn Abd-Allah, daga babansa, cewa Annabi Muhammad SAW ya ce wa babansa, “Abdullahi zai kasance mutumin kirki idan ya yi sallar tahajjudi (sallar Dare). Salim ya ce: "Bayan haka Abdullahi ba ya yin barci da daddare sai dan kadan a lokaci guda." Abdullah yana da shekara 18 a karshen rayuwar Annabi Muhammad SAW a shekara ta 632.
Abdullahi Ibn Umar (RA) ya koyi darasi daga babban malami Annabi Muhammad (SAW). Abdullahi (RA) ya kasance yana lura da bin diddigin duk wata magana da ayyukan Annabi (SAW) a yanayi daban-daban kuma ya kasance yana aiki da abin da ya kiyaye sosai da kuma ibada. Misali, idan Abdullahi (RA) ya ga Annabi (SAW) yana yin Sallah a wani wuri, sai ya yi salla a wuri daya. Idan yaga Annabi (SAW) yana addu'a yana tsaye, shima yayi addu'a yana tsaye. Idan ya gan shi (SAW) yana addu’a yana zaune, haka ma zai yi.
A’isha (RA) ta lura da wannan sadaukarwar da Abdullahi (RA) ya yi wa Annabi (SAW) sai ta ce:
“Babu wanda ya bi tafarkin Annabi (SAW) a wuraren da ya sauka kamar Ibn Umar”.
Duk da kiyaye ayyukan Annabi (SAW) da yake yi, Abdullahi (RA) ya kasance mai tsananin taka tsantsan, har ma da tsoron bayar da labarin fadin Manzon Allah (SAW). Sai dai idan ya tabbata cewa ya tuna kowace kalma ta hadisi ce kawai. Wani daga cikin mutanen zamaninsa ya ce:
"A cikin Sahabban Manzon Allah (RA) babu wanda ya fi yin taka tsantsan wajen karawa ko ragi daga hadisin Annabi kamar Abdullahi dan Umar."
Hakazalika, ya kasance mai tsananin taka tsan-tsan da rashin son yanke hukunci (fatawa). Da wani ya zo masa yana neman a yanke masa hukunci a kan wani lamari, sai Abdullahi bn Umar (RA) ya ce:
"Ba ni da wani ilmi ga abin da kuke tambaya." Sai mutumin ya ci gaba da tafiya sai Abdullahi (RA) ya tafa hannuwa cikin murna ya ce a ransa: "An tambayi dan Umar abin da bai sani ba, sai ya ce: Ban sani ba."
Saboda wannan hali ya hakura ya zama ‘Qadi’ (Alqali) ko Halifa duk da cewa ya cancanta ya zama. Matsayin Qadi yana daya daga cikin manya-manyan ofisoshi da kima a cikin al'ummar musulmi da Kasa da yake kawo daraja da daukaka har ma da dukiya amma ya ki wannan matsayi a lokacin da halifa Usman bn Affan (RA) ya ba shi . Dalilinsa na yin haka ba wai ya raina muhimmancin matsayin Qadi ba ne, a’a saboda tsoron da yake da shi na aikata kura-kurai na shari’a a cikin abubuwan da suka shafi Musulunci. Sayyidina Uthman (RA) ya yarda da cewa ba zai bayyana hukuncinsa ba, don kada ya yi tasiri ga sauran sahabbai da dama da suka yi aikin alkalai da shari’a.
An taba siffanta Abdullahi bn Umar (RA) a matsayin “ma'abocin dare”. Ya kasance yana tsayuwar dare yana Sallah yana kuka da neman gafarar Allah da karatun Alqur'ani. Ga 'yar uwarsa Hafsah (RA), Annabi (SAW) ya taba cewa:
Abdullahi salihai ne idan ya yawaita sallah da dare" (Sahihul Bukhari: 7031).
Tun daga wannan ranar, Abdullahi (RA) bai bar Qiyamul Lail ba (yana yin addu'a da neman gafarar Allah baki daya) a gida ko a kan tafiya. A cikin dare ya natsu yana ambaton Allah da yawa, ya yi Sallah ya karanta Alqur'ani yana kuka. Kamar mahaifinsa hawaye na zubo masa a hankali musamman lokacin da ya ji ayoyin Alqur'ani mai girma. Ubayd bn Umayr (RA) ya ruwaito cewa, wata rana ya karanta wa Abdullahi bn Umar (RA) wadannan ayoyi:
"To, yãya (masu laifi zã su kasance a Rãnar ¡iyãma) a lõkacin da Muka zo da shaidu daga cikin kõwace al'umma, sa'an nan Mu zo da kai, kana shaida a kansu? a rãnar nan, dã ƙasa ta shãfe su, kuma bã zã su ɓõye wa Allah abin da ya faru ba." (Suratun Nisa 4:41-42).
Abdullahi (RA) ya yi kuka yana sauraren wadannan ayoyin har gemunsa ya jike da hawaye. Watarana yana zaune cikin wasu abokai na kurkusa sai ya karanta:
“Bani! ya tabbata ga wadanda suke rage mudu, wadanda idan za su karbi hakkinsu daga mutane sai su bukaci a cika su, amma idan suka kimanta ko auna duk abin da suke binsu, sai su bayar da abin da Abinda Bai kai mizani ba. Shin, ba su sani ba cẽwa lalle ne su, lalle ne ana tãyar da su a kan wani yini mai girma, rãnar da mutãne ke tsaye ga Ubangijin tãlikai? (Suratul Mutaffifin 83:1-6).
A nan ya ci gaba da maimaita “ranar da mutane duka za su tsaya a gaban Ubangijin talikai” akai-akai yana kuka har ya suma.
Takawa da sauki da karimci sun wanzu a wajen Abdullahi (RA) suka sanya shi mutum ne wanda sahabbai (RA) suke da kima sosai da wadanda suka zo bayansu. Yana bayarwa da karimci bai damu da rabuwa da dukiya ba ko da kuwa shi da kansa zai fada cikin rashi sakamakon haka. Ya kasance dan kasuwa mai nasara kuma amintacce a tsawon rayuwarsa. Ban da wannan kuma ya samu tallafi mai tarin yawa daga Bayatul-Mal wanda ya kan kashewa talakawa da mabukata. Ayyub bn Wail Ar-Rasi (RA) ya ruwaito wani lamari na karamcinsa:
Wata rana Ibn Umar (RA) ya karbi dirhami dubu hudu da bargo na karammiski. Washegari Ayyub ya gan shi a cikin 'Suq' (Tufafin Larabci na gargajiya na maza) yana siyan abinci ga rakuminsa a kan bashi. Sai Ayyub (RA) ya tafi wajen iyalan Abdullahi ya ce:
Shin jiya Abu Abdur-Rahman (ma'ana Abdullahi bn Umar) bai samu dirhami dubu hudu da bargo ba?"
"Eh, lallai," ya Samu! suka amsa.
"Amma na gan shi yau a cikin 'Suq' yana siyan abincin rakuminsa, ba shi da kudin da zai biya." Ayyub yace.
“Kafin magariba jiya ya Rabu dasu, sanda ya dauki bargon ya jefa a kafadarsa ya fita, bayan ya dawo babu komai sai muka tambaye shi, Sai ya ce ya ba shi ga talaka,”
Abdullahi bn Umar (RA) ya kwadaitar da ciyarwa da taimakon gajiyayyu da mabukata. Sau da yawa idan ya ci abinci, akwai marayu da talakawa suna cin abinci tare da shi. Ya tsawata wa ’ya’yansa da yadda suke yi wa masu hannu da shuni da rashin kula da talakawa. Ya taba ce musu: “Kuna kiran masu kudi ku bar talakawa”.
Ga Abdullahi (RA) dukiya baiwa ne ba Uwargida ba. Hanya ce ta hanyar samun buƙatun rayuwa, ba don samun abubuwan more rayuwa ba.
Maymun bn Mahran yana cewa: "Na shiga gidan Ibn Umar, na kiyasta komai na gidansa ciki har da gadonsa, da bargonsa, da kafet dinsa da duk abin da ke cikinsa, abin da na samu bai kai dirhami dari ba."
Ba don Abdullahi bn Umar (RA) ya kasance talaka ba ne: lallai shi mawadaci ne. Ba don ya kasance baƙon abu ba domin lalle shi mai karimci ne kuma mai Tawali’u.
Da jimillar ruwayoyi 2,630, Abdullahi bn Umar (RA) shi ne na biyu mafi yawan riwayoyin hadisai. An ce ya yi taka-tsan-tsan da abin da ya ba da labari, ya na ba da labarin idanunsa cike da kwalla.
Duk da irin girmawa da dukkan musulmi suke masa duk kuwa da shawarar da aka yi masa na tsayawa tsayin daka wajen neman Qadhi ko halifa, ya nisanta kansa gaba daya daga wadannan tayin kuma a tsawon wadannan shekaru, ya jagoranci rashin son kai. da rayuwar takawa.
Ya rasu a Makkah shekara ta 74 (692 miladiyya) yana dan shekara 87.
Allah ya jikan Abdullahi bn Umar (RA) kuma ya yarda da shi, ya kuma tara mu a cikin tawagarsa.