Tallata Tsaraicin Ƴaƴa Mata Na Ɗaya Daga Cikin Hanyar Fara Zinace-Zinace Ga Ƴaƴa Maza




Shin har sai zuwa yaushe ne wasu ƴaƴa matan za susan cewa Cikar darajar su shi ne lulluɓe wannan tsaraicin da su ka mayar da shi abin ado a yanzu? 


Dalilin bayyanar da tsaracin ki‚ kin san adadin mutanen da suka yaba surar jikin ki? Dalilin bayyanar da tsaracin ki‚ kin san adadin mutanen da suka yi sha’awarki da burin sai sun keta miki Haddi ko ta wani hali? Dalilin bayyanar da tsaracin ki‚ kin san adadin mutanen da suke shauƙin tunanin surar jikin ki? Dalilin bayyanar da tsaracin ki‚ kin san adadin mutanen da suke yabon gaɓa-gaɓa na sha shin jikin ki? Dalilin bayyanar da tsaracin ki‚ kin san adadin mutanen da suka fara sha’awar fara Zina dake? Dalilin bayyanar da tsaracin kin san adadin mutanen da su faɗa irin wannan rayuwar na tallata tsaraici ga duniya a social media? Kin zama abin koyin su wurin yaɗa baɗala.


Kuma duk domin a samu followers da zama celebrity Duniya ta sanki. To Albishirin ki‚ duk wanda ya zama kece sanadin saɓon mahalicin sa‚ kina da kason zunubin baɗalan da ya aikata‚ domin sanadin ki ya saɓama Allah ta’ala. Duk tarin fillowers ɗin nan‚ da mutanen da suka sanki a duniya wurin tallata tsaraicin ki‚ zai yi wuya su miki addu'a koda sau ɗaya ne in kin mutu. Saboda kin yi suna a duniya ta hanyar saɓon Allah da ta’ata da lalata tarbiyyar al’umma. Abin tambaya anan shi ne‚ miye ribar tallata tsaraici ga duniya? Na’am ana samun kuɗi‚ amma wannan kuɗin sunan su Haram domin ba ta hanyar Halal aka samesu ba‚ koda kuwa za ki gina masallaci a yi sadaka da kuɗin yana cikin haramci domin kuɗin sunzo ne ta Haramtacciyar hanya.


Al’umma da yawa sun fara shiga harkar zinace-zinace ne‚ dalilin tallata tsaraici da ake yi a wannan zamanin. Ɗan ƙaramin yaro yasan waye mace? Haƙiƙa idan kin kasance ɗaya daga cikin masu tallata tsaraici a Social Media koda ta hanyar rashin sanya Lulluɓin da ze rufe tsaracin ki ne‚ ki sani kuna zaluntar Salihan matan da ko ƙunsin su‚ basa bari wanda ba shi da hurumin gani ya gani. Domin kema mace ne sunan ki a zahiri‚ a baɗini ba lallai ki amsa sunan ki mace ba‚ domin kina yin aikin da bashi daga cikin siffar Mata. Kece mace kinfi kowa sanin kanki‚ don haka kin san mene ne ake kira tsaraici a tattare dake? Amma ba lallai kisan ke halitta ce mai daraja ba‚ har sai kin ki yaye wannan tsaracin naki, sannan za ki fara sanin ke Halitta ce mai daraja.


 Allah ya ƙara sanya kunya a cikin zuƙatan ƴaya mata ƙanne da yayyi da iyaye baki ɗaya.


 Daga Ibrahim Y. Ibrahim

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post