Wanene Sayyidina Umar ?
Shine Umar Dan khadabi Dan Nufailu Bakuraishe, Ana Masa Alkunya Da Aba Hafsa, Mahaifiyarsa Hantamatu Bintu Hashim Dan Mugiratu.
Sayyidina Umar Yana Daga Cikin Sabiqina a Musulunci, Yana cikin Asharatu Biljanna, Na 2 Khalifa ga Musulmai Bayan Wafatin Annabi SAW, farkon Wanda Akayimasa Laqabi Da Amirul Muminina.
Annabi SAW yace: ”Umar Fitilar 'yan Aljanna".
Haihuwar Sa
An haifeshi a Makka Bayan Shekarar Giwa Da Shekara 13.
Musuluntarsa
Ya Musulunta Acikin Watan Zulhijja Shekara 6 Daga Annabata a Lokacin Yanada Shekara 26, Ya Musulunta Bayan Mazaje 45 Da Mata 11.
Ibn Abbas yace: Lokacin Da Sayyidina Umar Ya Musulunta Jibrilu Yasauka, Yace: Ya Annabi Muhammad SAW Halittun Sammai Suna Can Suna Farin Ciki Da Musuluntar Umar.
Darajarsa
Kadan Daga darajarsa
Sayidina Umar Yana Musulunta (RA), Musulunci Yakara Daukaka, Yayi Hijira a Bayyane, Ya Halarci Dukkan Yakoka Tare Da Annabi SAW.
Farko Khalifa Da Aka Fara kira Da Amirul Muminina, Farkon Wanda Yafara Rubuta Tarihin Hijira, farkon Wanda Yatara Mutane Akan Sallar Tarawihi.
Yabude Iraki, Busra, Farisa, Mausul, Misra Da Askandariya, Shine Farkon Wanda Yafara Mubayi'a ga Sayidi Abubakar.
Annabi SAw Yace : Da Akwai Wani Annabi Bayana Da Yakasance Umar Dan Khadabi ne.
Tawaliunsa
Yakasance Mai Tsoron Allah Da Adalci, Mai Yawan Azumi Da Tsayuwar Dare Idan Yana Limantar Mutane Sallah Zakaji Sautin Kukan Sa.
Siffarsa
Jismiya Yakasancr Mai Tsawo, Farine Da Ja, Idan Yana Tafiya Kace Yana Akan Abin Hawa Yake.
Siffa Ta Dabia Mai Adalci, Da Tausyi, Mai Kaifin Hankali, Mai Cikakkiyar Imani Bayada Hassada ga Kishin Musulunci.
Wafatinsa
Yayi Wafati Yana Da Shekara 63 Ranar Laraba 23 ga Zulhijja.
An birneshi Ranar Lahadi Adakin Nana Aishatu RA, Ya Zauna a Khalifa Shekara 10 Da Wata 6.
Wallahu A'alamu