Ga wasu sirrika guda 13 da mace za ta iya mallake miji dasu ko kuma shi miji ya mallake matarsa. Ga abubuwan kamar haka;
1. Yana da kyau ka/ki kasance kullum cikin gano abin da mijinki/matarka yake/take so da abinda Baya/bata so.
2. ki/ kasance Mara kwadayin abin hannusa ki Kama sana'a.
3. ki/ka kasance cikin tsaftace muhalinki da jikin ki/ka.
4. ki/ ka kula da iyayen ta/sa da yan'uwan ta/sa.
5. ki kasance mai tsoron Allah cikin dukkanin al'amuranki.
6. kada ki zama mai yawan shige-shige na makota.
7. ki Sani cewa, kece inuwar hutawarshi da jin dadinshi.
8. Idan mai Mata kika aura Kiyi biyayya ga matarsa, kada ki ce wai lokaci daya zaki raba shi da uwargida ki rike masa ya'yansa kamar ya'yan ki.
9. ki kasance cikin gano wani sabon salo-salo na wasanni a tsakaninku.
10. ki kasance kullum a jikin mijinki ki dinga nuna masa a kullum ke yarinya ce kina yi masa shagwaba.
11. kada ki dinga yin aikin da da namiji yake yi ya zama na kullum da an ganki an ga ya mace.
12. kada mijinki ya gano kina da mita ko saurin fushi.
13. kada ki zama mai bayyana sirrinki/ka (
social media) da kawaye ko iyaye ko yan'uwanki.
Ka zamo mutum mai nutsuwa kar ka sake ka rinka aikata abubuwan da za su jawo maka zubewar mutuncin ka ya kuma jawo zubewar mutuncin iyalanka kamar shaye-shayen.
Hakika shaye-shayen yana jawo raguwar kima da kuma yawan alfasha ya kasance ba ka da aiki sai zagi don akwai wadanda zagin ya zama musu riga ya zame musu jiki, ko zance za su yi sai sun hada da alfasha kunga ai wannan ba tarbiya bace ta gari idan baka so ya'yan ka su dauka sai ka daina.
Shawara ga ma'aurata mata
kiji tsoron Allah ki kula da mijinki, ki ba shi kulawa ta musamman ki zama mai tsafta da iya ado, ki zamo mai kisisinar da gwalli, da rangwada duk hanyar da zaki bi, ta haka zaki dauke hankalinsa ya daina kula yan'mata da zawarawa a waje.
Amma kin kasa kula da shi kin kasa kula da kanki, ba ki San me zai ja hankalin mijinki ba, kin zauna daga ke sai dauri iya kirji, ba wankin baki ba gyaran ga shi, ba kula da kafa ba wanki ba wanka ba aski hammatarki bare na gaba ( farji ) dole ki samu matsala don haka ki gyara in kina so ki ga dai-dai.
Ki zamo mace ta gari ta kwarai ki zamo mai samawa mai gidanki farin ciki karki sa masa tashin hankali da bacin rai karki zagi mijinki karki yi abinda zai bata masa rai
Musamman wajan kwanciya wasu matan suna azabtar da mazajensu ta wannan hanya wata in bai neme taba ba zata Kai kantaba wai ba aji, waya gaya miki kyaje wajen Jan ajin matsa sha'awa ko bai niyyar yi ba yaji yana bukarta yayi kuma ta haka hankalinsa zai dawo jikinki ko yaushe yaji yana so ya kasance da ke ki kula garin Neman gira a rasa Ido.
Da fatan kun ilimantu kuma da fatan za ku yi abubuwan da suka dace domin samun zaman lafiya tsakanin ku.