Da farko dai Genital wats wasu Nau'in abubuwa ne da suke fitowa mutum Musamman a bangaren al'aura na mace ko namiji, kuma suna iya fitowa a wani bangare na sassan jiki.
Sannan wannan ciwo kwayar cuta wacce ake kira da human papillomavirus (HPV). ita ce take haifar da ita, sannan kuma ana daukar cutar ne ta wajen jima'i domin itama tana cikin dangin Cututtukan da ake dauka wajen jima'i wato Std ko sti.
Wannan ciwo yana fitowa mace haka nan Namiji sannan wajajen da yafi fitowa sune:
1. Kan al'aurar Namiji (Azzakari)
2. Dubura
3. Gefen mara
4. Cikin farjin mace ko wajen sa.
Da dai sauran su.
Sannan suna jawo kaikayi ko jin zafi a wajen da suka fito, bangaren Namiji haka nan mace.
Hanyar da ake magance wannan matsala shine mutum yayi magani bangaren wanda zai sha domin kashe wannan virus din ta ciki, sannan ayi wanda za a shafa domin kashe na waje.
Hanyoyin da za a bi sune kamar haka :
1. A samu Tea tree oil ana samu a Islamic chemist za a debi karamin chokali sai a hada da man kwakwa babban chokali a waje daya, sai a rika safawa iya wajen da abin yake shafawa ake ba a sha.
Hanya ta biyu.
A samu tafarnuwa a samu kwaya daya sai a bare ta a yanka kamar gida 4 a dauki kaso daya a rika digawa a wajen idan za a kwanta zuwa safiya sai a cire.
Ko kuma a samu man tafarnuwa a rika shafawa a iya wajen idan za a kwanta barchi.
Dukkan wadannan hanyoyi za a yi su ne na tsawon sati 3 zuwa wata daya, Amma duk wacce ka dauka a ciki lokacin amfani da ita kaji yawan kaikayi ko rashin jin dadi a wajen to a ajiye ta ka daina.
Allah yasa a dace.
Sannan idan anyi wannan ba a samu waraka ba ayi kokari aga likita.