A Rana Mai Kamar Ta Yau 5 Ga Watan Mayu 2010 Allah Ya karbi Rayuwar Shugaban kasar Nijeriya Alhaji Umaru Musa 'Yar'adua, bayan fama da ciwon koda. Wanda aka fi tunawa da shi akan Ajanda Bakwai, ya nuna jagoranci na kwarai wajen zama shugaban kasa na farko a Najeriya da ya bayyana kadarorin sa.
An binne shi A Ranar 6 ga Mayu 2010, A Danmarina, Katsina.
Umaru Musa 'Yar'aduwa dan siyasar Najeriya ne wanda ya kasance shugaban kasar Najeriya daga 2007 zuwa 2010. An ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasar Najeriya da aka gudanar a ranar 21 ga watan Afrilun 2007, kuma an rantsar da shi a ranar 29 ga watan Mayun 2007.