Fitaccen jarumin masana'antar finafinan Kannywood, Ali Nuhu, ya bayyana yadda ƴaƴan sa suka ƙi zama jarumai a harkar fim.
Ali Nuhu ya ce burin sa ya ga ƴaƴan sa ana damawa da su a Kannywood, amma sai suka nuna akwai abinda suke son zama daban, ba harkar fim ba.
Jarumin ya ce bai damu ba, saboda yanzu zamani ya zo wanda ba a tilastawa yara abinda ake so su zama, a cewar sa goyon baya ake ba ƴaƴa akan duk abinda suke son zama.