Mutuwar aure a halin yanzu ta zama ruwan dare a tsakanin Hausa Fulani fiye da kowace kabila a duniya shakka-babu a kowace ranar Allah sai daruruwan ma'aurata sun rabu da juna saboda rashin jituwa da kan shiga tare da samun gindin zama a tsakanin su.
Meke Jawo Hakan?
Rashin bin ka'idojin zaman aure ne ke haddasa hakan? Ko kuma haka siddan ruwa yayi tsami banza?
Ya kamata mu duba wannan matsala yan'uwa maza da mata. 'Yar uwa ki rike matsayinki: a ko ina kika samu kanki ki tabbatar kin rike matsayinki na matar aure. wasu matan idan sun fita zuwa gidan biki ko suna da wuya su yi kama da matan aure wannan yana sa mazam banza su rika bin su wanda idan aka yi rashin sa'a matan masu kwadayi ne sai su rude ta har su kai ga aikata alfasha Allah ya kyauta.
Hadin gwiwa:
A matsayinki na matar aure akwai wasu ayyuka da suka kamata ki je ki yi tare da mijinki.
kyakkyawan zato:
A duk duniya babu miji da zaki same shi dauke da duk halayen da kuke so dole a samu wadansu kina so wasu kuma ba kya so.
Ki so mijinki yadda yake:
Wasu matan sai bayan aure sai su wayi gari su ga ba irin mijin da suke so ba ne, wasu don a ganinsu yana da kudi, wasu kuma halayensa ne ba sa so wannan matsala ce mai saurin kawo mutuwar aure wanda ya kamata ki so mutum dan Allah ba don abin hannusa ba.
A koda yaushe mijinki ya kira ki zuwa shimfidarsa, ki nuna masa farin cikinki, amma kafin ki kusance shi, ki tabbatar kina cikin tsabta domin wannan matsala ce ga mafi yawan mata.
Ko yi sana'a, Kada ki dogara da yawan tambayar mijinki kudi domin rainaki zai yi, ki yi kokarin koyon sana'a kina yi yar'uwa.
Rashin Dawowar Maigida Da Wuri.
Wannan Shawarwarin za su yi matukar taiamakawa mace don mallakar miji.
Ki sani mafi yawa daga mazaje sun fi son zaman waje akan zaman cikin gida, wannan wani abune da ya samo asali daga ainihin gundarin halayyar namiji don haka idan dai ba wani aikin laifi ne yake sa shi dadewa a waje ba to kiyi hakuri ki bi shi a hankali har Allah yasa ya rage dadewa a wajen sosai.
Ki daina jin haushin mijinki saboda wannan dabi'a, akan wannan dabi'a da yake da baki so matukar kina jin haushin abin kuma kina bayyana masa da jin haushin to wannan ba zai sa ya daina ba sai dai ya kara ingiza shi ma ga alkatawa.
Kar ki dinga damunsa da mita da korafin bai dawowa da wuri ba don namiji bayaso wannan.
Binciki kanki da yanayin zaman ku da shi bincike mai zurfi watakila akwai wani abinda kike yi mashi wanda yasa bai son zaman gida sai ki bincike da kyau.
Ki yi hakuri da namiji sai da hakuri zaman aure sai da hakuri.