Zaitun yana da amfani sosai da yake yi ga lafiyar dan adam wanda ba kowane yasan hakan ba. Shiyasa a yau na shirya kawo muku wasu daga cikin amfanin da yake dashi da ya dace ku sani. Ga su kamar haka ;
1. Kurajen Kazuwa.
Ga duk wanda yake da kurajen kazuwa ko wasu kuraje ko miki, ya samu ganyen zaitun ya kirbashi ya hada da garin habbatussauda ya rika shafawa a Wajen har ya warke.
2. Ciwon Kunne.
Ga duk mai fama da ciwon kunne, ya bari idan zai kwanta bacci sai ya hada man zaitun da na habbatussauda yana digawa a kunnen Insha Allah za’a samu saukin ciwon.
3. Cutar Kyasfi.
Duk mai fama da kyasfi a fuska ko a jikinshi sai ya samu ganyen zaitun busasshe, a daka shi ya zama gari sai a kwabashi da man zaitun, ya cakuda ya dinga shafawa Wajen da kyasfin yake Lokacin da mutum zai kwanta bacci sai ya wanke, insha Allah shima za’a dace.
4. Shafar Aljanu.
Duk mutumin da yake son ya rabu da Aljanu to ya rika yin amfani da man zaitun da habbatussauda saboda Aljanu basa son shi.
5. Ciwon Dan Yatsa Dan Kakkare.
Idan mutum yana fama da dan kakkare, ya samu man zaitun ya kwaba da lallen hausa, sai a karanta Ayatul kursiyyu sau bakwai a tofa a lallen a kuma tofa a hannun sai a kunsa lallen a hannun, insha Allah shima za’a samu waraka da ikon Allah.
6. Ciwon Nono.
Duk matar da ke fama da ciwon nono wanda ya toshe baya zuba to ana hada man zaitun da garinsa a shafa a nonon insha Allah kofofin za su bude.
7. Motsa Sha’awa Ga Ma’aurata.
Ga masu ƙarancin sha’awa man zaitun yana motsa sha’awa idan akayi amfani dashi lokacin da ake gabatar da wasa.
8. Ciwon Saifa.
Duk wanda yake fama da ciwon saifa, sai ya hada man zaitun da garin habbatussauda da zuma farar saka sai ya rika sha insha Allah za’a samu waraka.
9. Tsutsar Ciki.
Duk mutumin da yake da tsutsar ciki sai ya samu man zaitun da habbatussauda garin da zuma ya kwabasu ya rika sha Insha Allah za’a samu biyan bukata.
10. Gyambon Ciki (ulcer)
Duk mutumin da yake da gyambon ciki to sai ya samu garin habbatussauda Kamar cokali daya sannan ya samu garin kuma sari, da ganyen zaitun mai laushi yajikasu ya rika sha har sai ya warke.
11. Fitsarin Kwance
Duk yaron da yake da fitsarin kwance a samu garin zaitun da na habbatussauda a zuba a nono a rika bashi yana sha, zai daina da ikon Allah.
Wannan sune amfanin zaitun ke yi tare da magance cutuka ga lafiyar dan adam, da fatan kun ilimantu daga abubuwan da kuka Karanta.