Yana daga cikin suffar mace musulma ta ƙware shine takasance Mace wadda take da kishi.
In nace kishi ba ina nufin kishin nan da wasu suke fakewa dashi suna aikata ayyuka na rashin ɗa'a ga Allah da manzon sa ba.
Ba ina nufin kishin nan da wasu suke fakewa dashi su rika yin ayyuka na rashin imani ba, ba ina nufin kishin nan da yake ƙunshe da son rai da son zuciya da idon ka ya rufe komai za ka aikata saboda kawai ke kina jin kishi an zo anyi musharaka dake a gurin miji ba.
Kishin da sharia take so ki siffanta dashi shine,
Kiyi kishin kanki na farko a matsayin ki na musulma, ki yi kishin addinin ki, ki zamanto madubi kuma jakadiya ta Alkhairy akan addinin ki, karki aikata wani aiki da zai zamanto ya bayu zuwa ga a kushe addinin ki saboda kina kishin addinin ki.
Ki kishi akan mijin ki irin kishin da yake tabbatar da cewa kina kaunar mijin ki kuma kina biyar da rayuwar auran ki ta hanyar da Allah da manzon sa suke so.
Halitta daga cikin hallitun da Allah madaukakin sarki ya samar ko ɗabi'ar da Allah madaukakin Sarki ya samar acikin zukatan bayi akwai kishi aciki, daga bangaran maza da mata duka, to amma a bangaran mata tafi fitowa fili a bangaran mata tafi yawa.
To mace wadda tasan kanta, tana yarda cewa ita mai kishi ce, domin idan ba ta da kishi ma an samu matsala, duk matar da zata ce ni bani da kishi ni babu ruwana Kai (Malama tace Kai taja wata madda) Ku tuntube ta ɗayan biyu ne, ko dai kawai tana fadar abunda bashi ne gaskiya ba, ko kuma dai Al'amarin nan ne da ake cewa kan ba dadi.
Amma ba zai taba yiwuwar ba ace mace ba ta da kishi duk kankantar shi, To abunda sharia take so wannan kishin naki da kikeji a zuciyarki, na cewa ga wata tazo kuna rayuwa a karkashin inuwar aure ɗaya, kuna rayuwa a karkashin miji guda ɗaya to wannan soyowar da bakya so ta fiki a gurin miji, wannan kusancin da bakya so ta fiki samu a wurin mijin sai ya ingiza ki ya saka ki kasance cikin aikata abubuwan da miji zai yi farinciki dasu.
Biyyayar miji kamar yadda muka fada tun dazu (kafin ta fara magana akan kishi)
wajiba ce kuma ta samu ne bisa mai ? Umarni na sharia ba haka nan bane ba, dan haka idan kina yiwa mijin ki biyyaya karki ɗauka sai lokacin da ya ƙyautata miki sannan za ki yi mai, ba haka al'amarin yake ba,
ke wajibin ki daban shima nashi daban kowa kuma yana ƙoƙarin ya sauke nashi.
Don haka idan kina yiwa mijin ki biyayya sai ya zamanto ga wata abokiyar zama da kike ganin za ta fiki fada ta dan fiki shigewa kusa-kusa, kema sai hakan wannan kishin ya zamanto ya bayu izuwa game? Ya kara miki ƙaimi gun abunda zai janyo hankalin mijin ki akanki ya kara miki matsayi a wajen shi ya kara kusantar da dake shi, wannan bidda'i yana nuna cewa kina kara biyayya ne ga Allah ne madaukakin Sarki sai ki samu daukakar sha'ani da tarin lada a wajen Allah.
Amma wannan kishin na yawan faɗa ce faɗa ce na yawan ƙulle-ƙulle da makirce-makirce wasu ma har a zo a ringa raba hanya saboda duk fakewa da sunan kishi, wannan ba sunan sa kishi ba, wannan sunan sa kin baiwa zuciyar ki da sheɗan dama sun ci galaba a kanki, ya kan iya zaman towa akwai lokacin da za'a ɗan samu rauni irin raunin da yake samuwa ga ko wanne ɗan Adam.
Allah karawa rayuwar malaman mu Albarka
Daga Taskar Malama Zainab Ja'afar Mahmud Hafizallah