Muhimman Abu 3 Da Ya Zama Tilas Duk Namiji Yasani Game Da Matarsa - Android Pols




Ka dinga kula da yanayin matar ka, Ka kula da wadannan abubuwan guda uku kamar haka ;


(1) lokacin da take yin al'ada. Saboda wasu matan su kan yi ciwon baya, kai, musamman ciwon mara


(2) lokacin da take ɗauke da juna biyu: musamman farkon da ta samu cikin, wasu matan kanyi fama da matsanancin laulayi.


(3) lokacin da take naƙuda: wasu mata jini yakan tsinke musu da ka iya saka wa a rasa ɗa, uwar ko duƙƙansu. Domin haka a wannan lokacin mace na buƙatar kulawarka.


Akwai mazan da wallahi sai matan su suna cikin irin wannan halin sai su juya musu baya, daga bayan sun warke kuma babu kunya sai miji ya dawo yana tada jijiyar wuya shi mai mata, yana tinƙahon shifa namiji ne megidan.


Da fatan maza za su Kula da wadannan Muhimman abubuwan. 

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post