Akwai rashin kuzari na da namiji wanda daban yake da rashin karfin gaba. Rashin kuzari yana sawa mutum ba ya iya yin jima'i yadda ya kamata koda kuwa bashida cutar sanyi saboda bashida karfi.
Akwai kuma matsala ta rashin karfin gaba wanda shi sai idan anzo ana jima'i sai gaban yaki yin karfi wato ya kwanta ya lafke ya koma kamar lagwani.
sannan kuma ya zamto gaban karami ne ba ya iya yin abinda ya kamata yai. A duk lokacin da namiji zai sadu da mace gabansa yana kara girma ne saboda akwai wasu jijiyoyi da suke kara mishi girma.
Duk kankantar gaban namiji idan yana yin jima'i da mace a lokacin da yake cigaba da saduwa da ita a lokacin kuma gaban nashi yake kara yin ƙarfi, balle kuma ace lokacin da zai yi inzali lokacin ne gaban yake kara yin kumburi.
To ga masu fama da wannan rashin kuzari da rashin karfi da kuma kankanta, ga wani mai da zan baku ku dinga yin amfani dashi kuna shafawa a azzakarin ku idan zaku sadu da mace.
Ku yi kokari ku hada shi ko kuma idan kana da mata kasa ta hada maka shi sai kasamu roba mai murfi ko kwalba ka zuba a ciki.
Sai dai shi wannan hadin ba'a so idan an hada shi ya wuce kwana 5 ana amfani dashi domin kada ya samu matsala ya lalace. Ana so idan ka hada kayi amfani dashi na kwanaki 3 sai kuma ka kara wani daban.
A duk lokacin da za ka kwanta da iyalin ka sai ka dauko wannan maganin ka shafa shi a kan azzakarin ka, ko bushewar gaba ne da matarka to wannan maganin zai taimaka maka wajen shigar ta.
Duk rashin karfin gaban naka zai taimakawa jijiyoyin dake gabanka su tashi har ka biya bukatar ka.
Yadda zakai wannan hadin shine ka samu ayaba sai ka cinye ko ka yar ko kuma ka baiwa wani yaci, domin bawon ayabar ake da bubata. Amma anaso a samu wacce bawon nata ya nuna sosai sai ku samu turmi ku jajjaga shi.
Bawon ayaba guda 1 ya isa yaima kwana 3 kana amfani dashi. Idan kun jajjaga wannan bawon ayaba sai ku samu man Kadanya ku hada da wannan bawon ayabar da kuka jajjaga shi sai ku juye a kwalba ko roba a duk lokacin da kayi wanka zaka sadu da matarka sai ka shafa wannan man a gabanka sannan ka fara aiki.
Ka dinga yin wannan a duk sanda za kai jima'i, idan ya kare ka sake hada wani kana amfani dashi. Zakaga yadda kuzarin ka zai dawo kuma zakaga yadda gabanka zai kara karfi tare da jijiyoyin gaban naka.