Istimna'i : kalma ce ta larabci, wacce ke nuna jin dadi, ko halayyar jin dadi. Ma’anarta a anan kuwa shine, kalma ce da ake amfani da ita domin a nuna gamsuwa ta saduwa da ta faru tsakanin mutum da kansa. Ma’ana; mutum ne mace ko namiji ke amfani da hannunsa ko wata na’ura daban domin ya biya wa kansa bukata ta fuskar saduwa.
Duk da akwai cece-Kuce na masana da kuma manyan shehuna masu bincike kan kimiyya, kan shin Istimna’I yanada illa ko ba ya da illa. Wasu daga cikinsu, sun tabbatar da yanada illa a jikin dan Adam, yayin da wasu suke kokarin kare wannan mummunar dabi’ah, wacce ubangiji ya zarga a cikin Alqurani da cewa masu aikata hakan “yan ta’adda ne, masu ke ta iyakar da ubangiji ya shata musu, haka masana suka zargi masu aikata irin wannan dabi’ar.
Wannan dabi’ar yanzu ta girma, har ta kai a waya ake yin ta, inda za ka ga ko ka ji saurayi da budurwa suna saduwa da junansu ta waya, a yayin aikata hakan za ka ga suna wasa ne da sassan jikinsu, suna aikata wannan Istim’na’in har su biya wa junansu bukata.
Wasu Daga Hanyoyin Aikata Istimna'i, akwai hanyoyin da masu aikata suke bi daban-daban domin gamsar da kansu kamar haka ;
Haka ana amfani da wata na’ura domin aikata wannan aikin (vibrator)
Wasu sukan shafawa azzakarinsu sabulu, su dinga shafawa har su biya bukatarsu
Wasu sukan shafa mai su aikata hakan
Wasu sukan zuba yawu ko majina a azzakarinsu domin su ji saukin shafawa har su biya bukatarsu.
Duka wadannan suna faruwa ga maza, su kuma a mata suma akwai nasu salon hanyoyin da suke bi.
Mata Suna amfani da dan yatsa don su biyawa kansu bukata,
Suna amfani da azzakarin roba don su biyawa kansu bukata da sauransu.
Sai dai bincike ya tabbatar maza sun fi aikata wannan dabi'a fiye da mata, ko me ye dalili?
Daga Cikin Illolin Istimna'i sun hada da,
Kar mu manta na fada akwai sabanin malaman kimiyya kan; shin Istimna’I, yanada illoli, ko ba ya da? Ga kadan daga wasu illoli da na kalato daga bakunan masu bincike:
1. Yana Jawo Cutar Edema
Cutar Edema, ita ce cutar kumburar azzakari, yin Istimna’I na dan kankanin lokaci, kan haifar da wannan kumbura na azzakari, wanda yakan bace bayan ‘yan wasu kwanaki.
2. Laifi Ne
Ba addini ko al’ada da suka aminta da aikata Istimna’I, haka duk yadda mutum ya kai a rashin kunya, dole ya boye cewa shi mai aikata Istimna’I ne, idan haka ne kenan har masu aikata shi sun san cewa abin zargi ne kuma laifi ne.
3. Yana Jawo Prostate Cancer
Fitar da maniyyi sama da sau biyar a sati, musamman a mutane masu shekaru ashirin zuwa talatin suna da kaso 1/3 na kamuwa da prostate cancer fiye da wadanda basa yawan fitar da maniyyi, domin yawan yin Inzali (releasing) yana hana sinadarai da ke fada da wannan prostate cancer daga girma. Haka binciken 2003 da na 2008 suka tabbatar.
4. Rage More Saduwa
Yana rage more saduwa, amma wasu masana, suna ganin hakan tana faruwa ne kadai, a mazajen da ke matse azzakarinsu sosai a yayin wannan aikin. Suka bada hujjarsu kan cewa daga cikin amfanin Istimna’I akwai kara kwadayin saduwa.
5. Yana Saka Tsufa Da Wuri
Yawan fitar da maniyyi kan haifar da tsufa da wuri, musamman a wadanda ba sa cin abubuwa na gina jiki.
6. Wasu Daga Illolin Istimna'i
Bata ayukan mutum na wuni
Rasa makaranta
Rasa sabgar rayuwa
Taba mu’amular mutum
Mafita, hanyoyin da mutum zai kare kansa daga aikata wannan mummunar dabi'a
Mafita a wannan wasu abubuwa ne masu sauki kamar haka:
Mutum Ya Yi Aure : a lokacin da mutum ya yi aure, idan ya nufi ko ya kwadaitu da sha’awa, matarsa na kusa ko mijinta sai su biya wa juna bukata, galibi masu aikata wannan aikin marasa aure ne, kuma rashin aure yana daya daga dalilan da ke jefa samari da ‘yan mmata wannan aikin.
Yin Azumi: a koyarwar manzon Allah, ya umarci wani mutum mai yawan sha’awa da ya dinga yin azumi, haka ya koyar da mu cewa muyi aure, idan ba ma da halin yin aure mu samari, ya ce mu yi azumi domin kariya ce gare mu.
Shan Kanwa : kanwa tana rage karfin sha’awa, ga wanda ba ya iya yin azumi kuma ba kudin aure, sai ya dinga shan kanwa. Amma a guji yawan amfani da ita gudun ta kashewa mutum karfi gaba daya.
Ka Dinga Shiga Jama’a: idan mutum yana yawan shiga jama’a, ba yadda zai sami wani lokacin kebewa ya aikata Istimna'i.
Da fatan samari da yan mata za su kiyaye daga aikata wannan mummunar dabi'a.