Matsalolin Dake Faruwa Ga Sabbin Ma'aurata Idan Sun Yi Aure - Android Pols - Android Pols - latest news, natural remedies, and entertainment

Matsalolin Dake Faruwa Ga Sabbin Ma'aurata Idan Sun Yi Aure - Android Pols




Kaso 95 daga cikin 100 na matan da sukayi sabon aure suna fuskantar irin wannan matsalar.


Za kuyita soyayya da saurayinki, har kuyi aure cikin girmamawa da farin ciki, amma da lokacin da kukayi aure Idan ba ai sa'a ba yana fara kusantarki, zaiyi wahala kuyi sati biyu ko uku ko wata É—aya baki fara ganin canji daga yadda yake mu'amulantar ki ba.


Da yawan maza, da sun gama kwanciyar aure da matansu, shikenan itafa wannan matar batada wata daraja a gurinsa, kuma ba lallai taƙara ganin fara'arsa ba.


Idan kuwa kika ga yazo yana miki fara'a, to, yanada buƙatarki ne, kuma da zarar ya sami abinda yake nema saiya ƙara ɗaure fuska waishi bayasan a raina shi.


Maza masu irin waɗannan ɗabi'un akan samesu da ƙarancin tausayawa matansu, kuma suna da yawan saka mace aikin da yafi ƙarfinta.

Related Posts:


 Yaku 'Æ´an mata ku rinÆ™a roÆ™on Allah a cikin sujadarku ta ko wacce sallah, ta farillah ce ko nafilah, Allah ya azurtaku da mijin aure nagari, sannan kuma ku rinÆ™a sadaka.


Domin kuwa duk kyanki da zarar kin shiga gidan aure, to, shifa da ya kusanceki, na sati biyu ko wata É—aya, to zai daina ganin wannan kyan naki, 


Shiyasa Manzon ALLAH (S.A.W) yace: mai addini, kuma mai addininma kuma mai ɗabi'u na ƙwarai. Waɗanda kuma ke fuskantar irin wannan matsala muna roƙon Allah ya cusawa mazansu tausayinsu a cikin zuƙatansu.


Sannan ku yawaita istigfar da neman taimakon Allah, ku yawaita addu'a musamman a cikin sujadarku ta sallah dama dukkan wani gurare da ake amsa addu'ar bayi.


Allah ka yaye mana irin wanann masifu dake faruwa ga 'Æ´an uwanmu mata Ameen.


Allah ka azurta mazan da matan da kyautatawa juna a cikin zamantakewarsu Ameen.

Leave Comments

Post a Comment

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel